Wani Malami ya bayyana mulkin Buhari a matsayin cika umarnin Allah

Wani Malami ya bayyana mulkin Buhari a matsayin cika umarnin Allah

Wani Shehin Malami, Imam Kamarudeen Salawu ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari aikin Allah yake yi duk da irin dimbin matsalolin dake fuskantar Najeriya a wanann lokaci, inji rahoton jaridar Vanguard.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Salawu ya bayyana haka ne a yayin taron addu’o’i ga shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na 21, inda suke rokon Allah Ya bashi nasara a kokarinsa na neman zarcewa akan madafan iko.

KU KARANTA: Yadda binciken Sojoji ya kaisu ga bankado inda aka boye gawar janar Alkali

A yayin taron, Imam Salawu ya yi kira tare a gargadin mabiya addinai daban daban da su guji yin fatan samun miyagun shuwagabanni, wadanda zasu sayesu domin neman su tayasu da addu’an samun nasara a zaben 2019.

Wani Malami ya bayyana mulkin Buhari a matsayin cika umarnin Allah
Buhari
Asali: Facebook

A cewarsa: “Allah madaukaki ya bayyana a cikin Al-Qur’ani a suratul Taha, aya ta 20 cewa duk abinda dake sama da kassai nasa ne, da kuma duk abinda dake cikin kasa, Allah bamu san komai ba sai abinda ka sanar damu, kaine fiyayyen masani.

“Ya Allah ka shiryar damu hanya madaidaiciya, kuma ka amfanar damu daga abinda ka sanar damu, ka nuna mana shiriya ka bamu ikon binta, ka nuna mana bata ka bamu ikon guje mata.

“Miyagun mutane suna bayyana kawuanansu a matsayin mutanen kirkki, kuma suna kokarin saye mutanen Najeriya mabiya addinai daban daban da haramtattun kudade, Ya Allah ya kada ka basu sa’a akanmu, kuma duk masu shirin kada Buhari da kudaden sata su sani sun debo ruwan dafa kansu ne.” Inji shi.

Daga karshe Imam Salawu ya bayyana farin cikinsa da halartar taron addu’o’in, inda yace hakan ya nuna cewa Musulmai da Kiristoci ba makiyan juna bane, “Muna tare tsawon kwanaki 21 muna addu’o’i, zamu cigaba a hana har tsawon kwanaki 40 masu zuwa da ikon Allah don yi ma Najeriya addu’o’in alheri.”

Taron addu’o’in ya samu halartar sama da malamai 500 daga bangaren addinin Musulunci da na Kirista.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng