Shugaba Buhari ya kaddamar da bikin tunawa da yan mazan jiya da N10, 000, 000

Shugaba Buhari ya kaddamar da bikin tunawa da yan mazan jiya da N10, 000, 000

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da bukukuwan tunawa da yan mazan jiya, dakarun Sojojin da suka fafata a yakin Duniya na daya da na biyu da kuma yakin basasan Najeriya, kamar yadda Legit.com ta ruwaito.

A yayin kaddamarwar daya gudana a fadar shugaban kasar Najeriya, Aso Rock Villa, jim kadan kafin fara taron majalisar zartarwa shugaba Buhari ya saye shaidar mazan jiya da ake makalawa a riga, tare da basu gudunmuwar naira miliyan goma.

KU KARANTA: Kun barmu cikin mawuyacin hali – Sojojin Najeriya sun mayar ma Ministan Buhari martani

Shugaba Buhari ya kaddamar da bikin tunawa da yan mazan jiya da N10, 000, 000
Shugaba Buhari
Asali: Facebook

A tsarin tunawa da yan mazan, tun daga yau 31 ga watan Oktoba har zuwa 15 ga watan Janairu na shekarar 2019 ana bukatar manyan jami’an gwamnatin Najeriya da shuwagabanni da ma sauran yan Najeriya dasu daura shaidar nan a rigunansu a matsayin girmamawa.

Baya ga tunawa da wadanda suka fafata a yakin basasa, ana amfani da wannan biki don jinjina ma Sojojin dake aiki a yanzu. Daga cikin hidindimun da ake yi a yayin wannan biki akwai fareti daya kunshi Sojojin kasa, na ruwa, na sama da ma yan mazan jiya da suke raye.

Sauran sun hada da sakin tantanbaru a matsayin alamar zaman lafiya, girmama matattu daga cikin yan mazan jiya, harbe harben bindiga, addu’o’I a masallatan Juma’a da kuma manyan coci coci.

Shugaba Buhari ya kaddamar da bikin tunawa da yan mazan jiya da N10, 000, 000
Bikin tunawa da yan mazan jiya
Asali: Facebook

Daga cikin wadanda suka halarci taron kaddamarwar akwai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo, kaakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan Najeriya Winnifried Eyo-Ita.

Sauran sun hada da mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro, Babagana Munguno, sai kuma shugaban yan mazan jiya, Birgediya Janar Adakole Akpa mai murabus, wanda da hannunsa ya sagala ma Buhari da Osibanjo alamar tasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng