Rundunar Yansandan Najeriya ta yi ram da wasu miyagun barayin mutane 10 a Katsina

Rundunar Yansandan Najeriya ta yi ram da wasu miyagun barayin mutane 10 a Katsina

Rundunar Yansandan jahar Katsina ta sanar da kama wasu gungun gagga gaggan masu garkuwa da mutane da suka addabi al’ummar jahar Katsina, bayan sun yi ma wani mutumi, Abdulbasir Jargaba fashi a garin Funtua tare da yin awon gaba da dansa mai shekaru 8, inji rahoton Punch

Majiyar Legit.com ta ruwaito rundunar Yansandan ta bayyana sunayen yan fashin kamar haka Hussaini Abdullahi, 42; Ibrahim Umar, 60; Abubakar Idris, 20; Samaila Abdullahi,28; Saidu Ibrahim 20, Halidu Ibrahim, 30, Shaibu Maikudi, 20; Ibrahim Alhasan, 45, Mohammed Adamu, 22 da Shehu Lawal, 32.

KU KARANTA; Karancin albashi: Ku tara kayan abinci kafin mu fara yajin aikin dindindin a ranar 6 ga watan 11 - NLC

Da yake bayyana miyagun mutanen ga manema labaru a babban birnin tarayya Abuja,, kaakakin rundunar Yansandan Najeriya Moshood Jimoh ya bayyana cewa sun kwato bindigu kirar Ak-47 guda biyar, bindigar Pump Action guda daya da alburusai da dama daga hannunsu.

A cewar Jimoh: “A ranar 12 ga watan Agustan 2018 ne barayin suka afka cikin gidan Malam Abdulbasir dake garin Jargaba cikin karamar hukumar Funtua ta jahar Katsina, inda suka yi awon gaba da dansa mai shekaru 8, Abdulazeez Basir, suka rike shi na tsawon kwanaki 11.

“Masu garkuwan basu sake yaron ba har sai da aka biyasu kudin fasa, sai dai wasu kwararrun jami’an Yansanda dake karkashin umarnin babban sufetan Yansandan Najeriya, IG Ibrahim Idris sun bi sawunsu har zuwa sansaninsu dake cikin dajin Birnin Gwari.

“Anan ne jami’an Yansandan suka samu nasarar cafkesu bayan wata doguwar karanbatta ta musayar wuta da suka kwashi tsawon lokaci suna yi.” Inji kaakakin Yansanda Jimoh Moshood.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan Najeriya ta kama wasu yan bindiga dake fitinan matafiya masu bin safara akan hanyar Kaduan zuwa Abuja, da hanyar Kaduna zuwa jahar Neja.

Yansanda sun kama yan fashin ne da suka hada da Adamu Dahiru da Lawali Abubakar, a mabuyarsu dake tsakiyar dajin Madaro, cikin karamar hukumar Birnin Gwari ta jahar Kaduna, sa’annan sun ceto mutanen da suka yi garkuwa dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel