Buhari ya gana da 'yan takarar APC

Buhari ya gana da 'yan takarar APC

A jiya, Talata, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da daukacin 'yan takara a karkashin inuwar jam'iyyar APC a fadar sa da ke Abuja.

Da yake gabatar da jawabi ga 'yan takarar, shugaba Buhari ya roki wadanda su ka yi fushi da jam'iyyar APC da kar su fita.

Kazalika ya yiwa 'yan jam'iyyar da ke fushi da ita alkawarin cewar zai saka baki domin ganin uwar jam'iyya ta bawa mai hakki hakkinsa.

Jigo a jam'iyyar APC, Ahmed Wadada, ya yi jawabi ga manema labarai, amadadin ragowar 'yan takarar, bayan sun kammala wata ganawar ta sirri.

Ya bayyane cewar mambobin jam'iyyar sun yi alkawarin yin aiki tare bisa gaskiya da rikon amana domin samun nasarar APC a zabukan 2019.

Buhari ya gana da 'yan takarar APC
Buhari ya gana da 'yan takarar APC
Asali: Twitter

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar gwamnonin APC da har yanzu ke fushi da yadda zabukan fidda 'yan takara su ka gudana a jam'iyyar za su yi taro, gabanin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, a Abuja.

Majiyar jaridar Daily Trust ta rawaito cewar gwamnonin za su yi taron ne domin nuna bacin ransu bisa yadda aka gudanar da zabukan cikin gidan jam'iyyar a jihohinsu.

DUBA WANNAN: Kare jini biri jini: Mabiya Shi'a sun cinnawa motar 'yan sanda wuta a Abuja a sabuwar zanga-zanga, hotuna

An fuskanci matsaloli a jihohi irin su Zamfara, Imo da Ogun a zaben fidda 'yan takarar kujerar gwamna.

Daga cikin gwamnonin da su ka nuna kin amincewar su da zaben fitar da 'yan takara da uwar jam'iyyar APC ta yi akwai gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu; gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow; da na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i.

Jarida ta bayyana cewar shawarar gwamnonin na yin taron shine tattauna yadda za su tabbatar da cewar 'yan takarar da su ke so ne kawai za su yi takara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng