Yadda muka kama 'yan Shi'a dauke da bama-bamai - 'Yan Sanda

Yadda muka kama 'yan Shi'a dauke da bama-bamai - 'Yan Sanda

Hukumar 'Yan sandan Najeriya na babban birnin tarayya, Abuja da sanar da cewar da kama wasu 'yan kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) dauke da bam din kwalba hade da man fetur 31 da ma wasu muggan makamai da suke shigowa Abuja.

Hukumar ta ce 'yan Kungiyar sun shirya makircin zuwa kai hari ne kan al'umma da kuma jami'an hukumomin tsaro da ke aikin kiyaye rayyuka da dukiyoyin al'umma a Abuja.

Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin Kwamshinan 'yan sanda na Abuja, Bala Ciroma yayin wata taron manema labarai da ya kira.

Yadda muka kama 'yan Shi'a dauke da bama-bamai - 'Yan Sanda
Yadda muka kama 'yan Shi'a dauke da bama-bamai - 'Yan Sanda
Asali: Facebook

"A ranar 30 ga watan Oktoban 2018 misalin 12:30 na rana ne jami'an 'yan sanda da ke Tipper Garage a Katampe suka kama wani Mustapha Abdullahi mai shekaru mazaunin Unguwan Gwari a Suleja dauke da bama-baman kwalba da ake kerawa da man fetur guda 18 boye cikin jakar sanya kaya.

DUBA WANNAN: Soji sun fadi adadin mutanen da suka rasu sakamakon rikici da 'yan Shi'a a Abuja

"Matashin ya yi basaja ne cikin fasinjojin mota inda ya yi niyyar shigar da bama-baman cikin babban birnin tarayya Abuja amma asirinsa ya tonu yayin da yan sanda suka bincike kayan da ke jakar kuma suka kama shi nan take.

"Sauran abubuwan da aka samu tare da shi sun hada da wukuke biyu da lighter. Za a gurfanar da shi a gaban kuliya da zarar an kammala bincike," inji Ciroma.

Kazalika, duk dai a ranar 30 ga watan na Oktoba, yan sandan sun kama wani Abdullahi Umar mai shekaru 22 da ke zaune a Gadan Karte a karamar hukumar Illela ta jihar Sakkwato dauke da wasu bama-baman guda 13.

Bayan an masa tambayoyi ya bayyana cewar ya taho daga Sakkwato ne domin ya hadu da sauran 'yan kungiyar Shi'a domin su cigaba da gudanar da zanga-zangarsu. Shima za'a gurfanar da shi a kotu bayan an gama bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164