Jawabin shugaban kasa Buhari a yayin ziyarar jaje da ya kai jahar Kaduna

Jawabin shugaban kasa Buhari a yayin ziyarar jaje da ya kai jahar Kaduna

A ranar Talata 30 ga watan Oktoba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar jajantawa ga al’ummar jahar Kaduna, bisa rikicin daya barke sau biyu a cikin sati biyu, wanda ya janyo asarar dukiya da rayukan mutane 75.

Legit.com ta ruwaito shugaba Buhari ya bayyana bacin ransa da tashe tashen hankula da ake yawan samu a jahar Kaduna, musamman na kwana kwanan nan daya faru a kasuwar magani da kuma cikin garin Kaduna, don haka ya bukaci ganin an kawo karshen rikicin.

KU KARANTA: Rai bakon duniya: Yadda tsawa mai karfi ya halaka wani Uba da dansa

Haka zalika Buhari ya umarci rundunar Yansandan Najeriya da ta kara sa ido musamman game da hanyoyin da miyagun mutane ke bi wajen tayar da rikici domin kare al’umma, sa’annan ya bukaci da rundunar ta zage damtse wajen gurfanar da masu laifi gaban kotu.

Jawabin shugaban kasa Buhari a yayin ziyarar jaje da ya kai jahar Kaduna
Buhari
Asali: Facebook

Bugu da kari a yayin taron da ya samu halartar sarakunan gargajiya, shuwagabannin addini, kungiyoyin kabilu, shugaba Buhari ya rokesu dasu kara matsawa cikin al’ummansu, kuma kada su kuskura su baiwa miyagun mutane kariya a duk lokacin da jami’an tsaro ke nemansu.

Game d kisan Agom adara kuwa, Buhari yace: “Ina taya iyalai, yan uwu, abokan arziki, yan kabilar adara da ma gwamnatin jahar Kaduna ta’aziyyar Agom Adara, Maiwada Galadima, mutum ne da yayi suna wajen bayar da shugabanci nagari ga jama’ansa, mutumin kirki abin koyi.” Inji shi.

“Na yaba kwarai da yadda gwamnatin jahar Kaduna ta shawo kan rikicin ba tare da bata lokaci ba, zamu cigaba da taimaka ma gwamnatin da Karin jami’an tsaro don kara tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jahar, za kuma mu cigaba da daukan matasa aikin tsaro tare da watsasu sassan kasarnan don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Ina kara yaba ma gwamnatin jahar Kaduna da kananan hukumominta bisa matakin da suka dauka na kara yawan ofisoshi da sansanin jami’an tsaro a duk wuraren da akwai yiwuwar samun tashin tashina a fadin jahar, don haka ya kamata su ma jama’an jahar Kaduna su bada nasu gudunmuwar wajen tabbatar da zaman lafiya, tare da warware sabaninsuta hanyar sulhu.” Inji shi.

Daga karshe Buhari yace an san jahar Kaduna a matsayin gidan Sardauna, kuma gidan sabuwar Najeriya, don haka bai kamata jama’an garin su bari a sake mata suna ba zuwa gidan rikici. Daga cikin wadanda suka halarci taron Sarakuna, kungiyoyi, akwai manyan jami’an gwamnati, yan siyasa da manyan jami’an tsaro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng