Wani da jirgi ya tashi ya barshi ya fashe da kuka bayan da jirgin yayi hadari kowa ya mutu
- Jirgin ana sa rai ya kashe mutane 189 a Indonesia a karshen mako
- Ya gagara zamun tafiya saboda go sulo da ake a hanya
- Yanzu shi kadai yayi rai cikinsu duk

Asali: Twitter
Sony Setiawan, ya ji babu dadi, bayan da jirgin Lion Air ya tashi ya barshi a karshen makon jiya, dauke da mutane 189, wanda shine cikon na 190 din.

Asali: Depositphotos
Go slow na motoci ne ya hana shi isa Iyapot da wuri, har aka gama chakin kowa ya hau jirgi aka rufe kofa.

Asali: Twitter
Sai dai jin kadan da jirgin ya tashi, sai ya sami tangarda, inda yayi kokarin dawowa tasharsa, amma ya gagara a hanya, har dai ya sullubo ya fado a ruwa, kowa kuwa ya mutu harda matuka jirgin.
DUBA WANNAN: Dan gidan Ghaddafi zayyi takara a Libya
Yanzu dai, da labari ya ishe masa cewa kowa a jirgin ya mutu, Sony Setiawan ya fashe da kukan dadi, da makokin yadda tsautsayi ya tsallake shi, amma ya tafi da sauran.
Ya hau wani jirgin ne daga baya, bayan da yayi godiya ga abar bautarsa kan tseras dashi daga wannan bala'i da tayi.
Mai rabon ganin badi sai ya gani...
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng