Jama’a sun cika wajen gangamin da Fasto Kumuyi ya shirya a Abuja
Mun samu labari daga Jaridar Leadership cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimin sa Yemi Osinbajo da wasu manyan kasar nan sun halarci taron da Fasto William Kumuyi ya shirya jiya.

Asali: Facebook
Babban Limamin cocin nan na “Deeper Christian Life” na Duniya watau Fasto William F. Kumuyi ya shirya wani gangami a babban filin wasan Najeriya da ke Birnin Tarayya Abuja a jiya inda Kiristocin Kasar su ka cika makil.
Shugaban Kasa Buhari ya tura Mai magana da yawun sa watau Femi Adesina a matsayin wakilin a a wajen taron. Sanatan Jihar Kuros-Riba Jon Enoh yana cikin manyan da su ka halarci wannan babban gangami da aka yi a Abuja.
Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya tura Rabaren Isaac Peter ne ya wakilce sa. Sauran wadanda su ka halarci wannan babban taro sun hada da Tsohon Mataimakin babban Gwamnan CBN na kasar nan Dr Obadiah Mailafiya.
KU KARANTA: Za a birne Matar Hameed Ali da ta rasu a babban Birnin Tarayya Abuja
Dr Jonah Samson na Kungiyar CAN tare da wasu manyan Limaman Kirista irin su Rabaren Dr Isaac Omolafe da Bishof Joshua Maikori Audu sun sa wa wannan taro albarka. Sauran Limaman Darikar duk sun halarci wannan taro.
Jagororin cocin “Deeper Christian Life” daga Jihohi dabam-dabam na kasar wadanda su ka hada da Raymond Egunjobi, Toyin Araromi, Andrew Osagie, Christopher Ogbagi, Femi Ade da Joshua Esho su na cikin wadanda aka gani.
Fasto Kumuyi yayi kira ga Kiristoci su tuba wajen Ubangiji su nemi gafara kuma ya nemi su sallama rayuwar su ga Yesu Al-masihu mai ceto inda ba a bar wurin ba sai da yayi wa jama'a addu’a ta karama.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng