Karin bayani kan gawar Janar Alkali da aka kashe a Dura-Du a Jos
- Ana cigaba da gano sabbin bayanai kan Janar Alkali da aka kashe a Dura-Du a jihar Plateau
- Hukumar soji ta damke wani kwarare da ya taimaka wajen canjawa gawar Janar din kabari
- Sojin kuma sun ce tana suna hujjoji da ke nuna cewa shugabanin yankin na da hannu a kisar
Hukumar Sojin Najeriya tana cigaba gano wasu sabbin bayanai game da bacewar Manjo janar Idris Alkali a yankin Dura-Du da ke karamar hukumar Jos ta Kudu na jihar Plateau.
Jami'an tsaro masu amfani da karnuka da ke gano inda aka boye abubuwa ta hanyar bin kanshi suna ta sintiri a sassa da dama na garin na Dura-Du wadda yawancin mazauni garin sun tsere.
Duk da cewa Hukumar Sojin Najeriya ta tabbatarwa al'ummar yankin cewar babu abinda zai same su, galibin mutanen garin sun kulle shagunansu kuma sun tsere daga gidajensu domin tsoron ko ta kwana.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: 2019: Yarabawa sunyi kaca-kaca da Fashola kan yiwa Buhari kamfe
Ta hanyar amfani da karnukan masu gano inda aka boye abubuwa hukumar sojin Najeriya suka gano wani kabari mara zurfi inda aka fara binne Janar Alkali mai murabus kafin daga baya aka sake dauke gawarsa zuwa wani wajen daban.
Babban kwamandan 3 Amoured Division ta Maxwell Kobe da ke Rukuba, Manjo Janar Benson Akinroluyo ya shaidawa manema labarai cewa mutane hudu da suka bayar da bayannan sirri a lokuta daban-daban sun kai sojin wani wuri da ke kira 'No man's land' inda aka gano kabarin.
Hukumar Sojin ta bayyana cewa an dauke gawar Alkali an canja mata waje da taimakon wani kwarare bayan Sojin sun gano motarsa da kayayakinsa a cikin kududufi.
"Kwararen da ya taimaka wajen canja wa gawar waje yana hannun hukuma wanda hakan ya nuna mutanen garin na kokarin yin rufa-fufa ne game da kisar gillar da aka yiwa Alkali.
"Akwai wasu hujjoji da ke nuna cewar akwai hannun shugabanin yankin wajen aikata wannan mummunar aikin," inji Janar Akinruloyo.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng