Naci dambun kuturu: PDP ta cigaba da zawarcin gwamnan APC da wasu mambobin jam'iyyar
- Jam'iyyar PDP ta sake mika goron gayyata ga gwamna Akinwumi Ambode na jihar Legas
- PDP tayi ikirarin cewar tana gayyatar 'yan jam'iyyar ne saboda rashin adalci da akayi musu a APC
- PDP ta shawarci 'yan jam'iyyar na APC suyi koyi da takwarorinsu a wasu jihohi da suka fice daga jam'iyyar bayan an hana su tikitin takara
Jam'iyyar adawa ta PDP reshen Jihar Legas ta sake yin kira da mambobin jam'iyyar APC da ke jihar su taho su hada karfi da karfe tare da PDP domin su ceto jihar daga hannun wani mutum daya da ke juya jihar.
PDP ta bukaci 'yan APC su shigo dare jirgin ceto Legas wato "free Lagos train" idan har su masu son cigaban jihar Legas ne da kuma kishin mutanen jihar.

Asali: Depositphotos
DUBA WANNAN: 2019: Yarabawa sunyi kaca-kaca da Fashola kan yiwa Buhari kamfe
PDP tayi wannan kira ne saboda yadda wasu mambobin jam'iyyar na APC suka rasa tikitin sake takara a jam'iyyar a zaben 2019 wanda ciki har da gwamna mai ci a yanzu Akinwumi Ambode.
A sanarwar da ta fito bakin mai magana da yawun PDP a jihar, Mr Taofiq Gani, ya shawarci mambobin APC na jihar Legas su bi sahun takwarorinsu na jihohin Ogun, Oyo, Kaduna, Imo da sauransu.
Gwamna Ambode ya rasa tikitin takarar ne bayan Jagora a jam'iyyar ta APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zabi wani dan takarar gwamna a jihar da zai maye gurbin Ambode wanda hakan ya tilasta Ambode hakura da takarar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng