An kashe mutane 6 a wani sabon rikici a cikin Jihar Zamfara

An kashe mutane 6 a wani sabon rikici a cikin Jihar Zamfara

Mun samu labari cewa an kashe mutane a wani hari da ‘Yan bindiga su ka kai Jihar Zamfara kwanan nan. An kai harin ne a wani Kauye da ake kira Gurbin Baure da ke cikin Karamar Hukumar Zurmi.

An kashe mutane 6 a wani sabon rikici a cikin Jihar Zamfara
Rahotanni sun ce harin yan bindiga ya lakume mutum 6 a Zamfara
Asali: Depositphotos

Wani babban Jami’in ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara DSP Muhammad Shehu ya bayyanawa gidan rediyon BBC Hausa cewa wasu ‘Yan bindiga da ba a san iyakar su ba sun dura Kayen Baure cikin tsakar dare inda su kayi ta harbin Jama’a.

Jami’an tsaro sun tabattar da cewa akalla mutane 6 ne su ka bakunci lahira bayan harin da aka kai a cikin Karamar Hukumar ta Zurmi. Daga cikin wadanda aka kashe har da wani Jami’in ‘Dan Sanda inji Kakakin Jami’an tsaro na Jihar.

KU KARANTA: Sanata Shehu Sani ya bankado sirrin Gwamna El-Rufai

Abubakar Muhammad wanda shi ne Mataimakin Shugaban Hukumar ta Zurmi ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa Jama’an Gari sun shiga cikin wani yanayi a halin yanzu yana kuma mai cewa wadanda aka kashe din sun wuce yadda ake tunani.

Ku na da labari cewa ba yau aka fara kai irin wannan munanan hare-hare ba domin kuwa an fi shekera guda ana kashe Bayin Allah a cikin wannan Gari na Zurmi. Wannan karo dai ‘Yan bingiga sun yi kone-kone bayan sun kashe Jama’a da dama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel