Tattakin Arbaeen: Artabu tsakanin mabiya Shi'a da sojoji ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2

Tattakin Arbaeen: Artabu tsakanin mabiya Shi'a da sojoji ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2

- Rahotanni sun bayyana cewar a kalla mutane biyu ne su ka rasa ransu bayan wani artabu tsakanin mabiya Shi'a da dakarun sojin Najeriya

- Jaridar Vanguard ta rawaito cewar an samu hatsaniya ne bayan sojojin da ke aiki a kan hanyar shiga Abuja sun hana mabiya Shi'ar wucewa

- A jiya, juma'a, ne kakakin kungiyar Shi'a ya sanar da 'yan jarida niyyar kungiyar na fara tattakin kwanaki uku daga ranar Asabar

Rahotanni sun bayyana cewar a kalla mutane biyu ne su ka rasa ransu bayan wani artabu tsakanin mabiya Shi'a da dakarun sojin Najeriya.

An samu hatsaniya tsakanin mabiya Shi'a da sojojin ne a unguwar Zuba da ke Abuja yayin da Shi'ar, daga Suleja, ke tattakin kwanaki uku (Arbaeen) zuwa Abuja.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar an samu hatsaniya ne bayan sojojin da ke aiki a kan hanyar shiga Abuja sun hana mabiya Shi'ar wucewa a daidai dutsen Zuma.

Tattakin Arbaeen: Artabu tsakanin mabiya Shi'a da sojoji ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2
Tattakin Arbaeen na mabiya Shi'a
Asali: Facebook

Hakan ya fusata mabiyan na Shi'a da har ta kai sun fara jifan sojojin da duwatsu, su kuma su ka bude ma su wuta, lamarin da ya kai ga asarar rayuka biyu.

A jiya, juma'a, ne kakakin kungiyar Shi'a ya sanar da 'yan jarida niyyar kungiyar na fara tattakin kwanaki uku daga ranar Asabar.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga cikin kakin soji sun hallaka shanun makiyaya fiye da 150 a Taraba

Kungiyar ta bukaci mazauna garin Abuja da kar su tashi hankalin su, domin fiye da magoya bayan Zakzaky mutum miliyan daya za su gudanar da zanga-zanga a garin.

A cikin jawabin da Kungiyar mabiya Shi'a (IMN) ya fitar a daren jiya, ta tabbatar da mutuwar mutane 2.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng