Rundunar Sojan Najeriya ta bayyana dalilin girke jami’an Sojoji a majalisar dokoki
Rundunar Sojan kasar Najeriya ta bayyana cewa dalilinta na girke dakarun sojojin Najeriya a kusa da majalisa shine don kare majalisar, fadar shugaban kasa da manyan kotunan dake tsakani daga afkawar yan shia.
Majiyar LEGIT.com ta ruwaito an samu karuwar adadin dakarun Soji dake sintiri a yankin majalisa, wanda hakan ya razana jama’a, musamman ma’aikata da yan majalisa, wanda suke ganin kamar Sojojin zasu kwace majalisar ne.
KU KARANTA: Allah kare masifa: Kwale kwale ya nuste da Babura 17, dan adam 20 a jahar Benuwe
Sai dai mataimakin daraktan watsa labaru na rundunar Sojan jasa, HT Tagwai ya musanta wannan rade radi, inda yace babu gaskiya cikin maganar wai suna kokarin kwace majalisar bane, yace an kara adadin Sojoji ne don gudun kada yan shia dake zanga zanga su fada majalisar.
Sa’annan ya kara da cewa ai an saba girke rundunonin Sojoji a wurare daban daban a babban birnin tarayya Abuja a duk lokacin da suka samu rahotanni sirri dake nuna akwai yiwuwar samun hatsaniya da rikici.
Jami’an tsaro sun samu rahotannin cewa yan shia zasu fada ma majalisa da kuma fadar shugaban kasa a zanga zangar da suke yi na ganin an sako musu jagoransu, Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda gwamnati ta kama shi tun a watan Disambar 2015.
“A cigaba da aikinmu na tabbatar da tsaro a wannan yanki, mun tura Karin adadin Sojoji ne sakamakon rahoton da muka samu cewa kungiyar yan Shia za ta afka ma yankin, don haka aka girke Sojoji don tabbatar da doka da oda.
“Muna sanar da kafafen watsa labaru su dinga tabbatar da rahotanni ko labaru kafin su wallafasu don gudun gurbata tunanin jama’a, rundunar Sojan kasa runduna ce dake da kima, kwarewa da sanin makaman aiki kamar yadda ake ayi a duk fadin duniya.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng