Makokin 40: 'Yan shia zasu fara machi zuwa zaria daga birane a qafa
- Shi'a ta nemi hadin kan yan sanda da kuma gwamnatin Kano akan tattaki da zata gudanar
- Duk wani farmaki da za'a kawo musu ya karya ka'ida
- Mun sanar da hukumar yan sanda saboda neman tsaro

Asali: Depositphotos
Kungiyar nan ta IMN wadda aka fi sani da Shi'a ta nemi hadin kan hukumar 'yan sanda da kuma gwamnatin jihar Kano a bisa tattaki da zasu gudanar don tunawa da limaminsu Usaini jikan manzo.
Zasu gudanar da tattakin ne zuwa hubbaren Imam Husain dake Iraki, wanda amma sukan kwatanta da zuwa Zaria Husainiyya, wadda tuni soji suka ruguje.
Kungiyar ta bayyanawa 'ya'yanta cewa zasuyi tattakin ne daga Kano zuwa hedkwatar su dake Zaria.
DUBA WANNAN: Zaman Lafiya dole ne a Kaduna - Hunkuyi
Mai magana da yawun kungiyar Dr Dauda Nalado da yake tattaunawa da yan jarida jiya a jahar Kano yace sun riga da sun sanar da hukumar yan sanda cewa zasuyi tattaki dan su samu tsaro.
Yace "muna bin doka a duk lokacin da muka fito yin ibadar mu,sannan duk wani farmaki da za'a kawo mana a yayin tattakin mu ya kauce wa ka'ida sannan a take mana hakkin mu na dan Adam".
Shekaru kusan 1,300 kenan ake wannan makoki da zub da jini, har yau kuwa ba'a gama ba, abin kuwa ya iso wa bakaken fata a Najeriya gadan-gadan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng