Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yan tagwayen Mata a Zamfara (Hotuna)
Har yanzu dai sai dai ace an samu sauki game da matsalar sace sace da kashe kashe da ake yawan samu a jahar Zamfara, inda a yan kwanakinnan ayyukan masu garkuwa da mutane da nay an bindiga sun sake farfadowa a sassan jahar.
Anan wasu yan bindiga ne suka yi garkuwa da wasu mata yan tagwaye, Hassana da Hussaina dake zama a garin Dauran, cikin karamar hukumar Zurmi, a ranar Talata 23 ga watan Okotoba, kamar yadda LEGIT.com ta ruwaito.
KU KARANTA: Wani Sanata daga babbar jahar PDP ya yi wankan tsarki ya fada jam’iyyar APC
A baya dai wannan matsala kamar ta kau, musamman a lokacin da dakarun Sojojin Najeriya da sauran jami’an hukumomin tsaro suka mamaye garin suna yaki da yan bindiga, inda suka samu nasara kamawa tare da kashe wasu gagga gaggan yan bindiga da suka shahara.

Asali: UGC
Da haka sai dai iyayen wadanda aka kama ko danginsu su yi ta cinikin kudin da zasu biya yan ta’addan domin su sako musu yan uwansu, idan kuma ba haka sai su yi barazanar kashe wadanda suka kaman, musamman idan an saka Yansanda a cikin maganar.
Sai dai ayyukan Sojojin ya lafa, don haka yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke cin karensu babu babbaka a yanzu, kuma Karin matsala shine ba’a samu rahotannin ta’asan da yan bindiga ke yi a yankin kafafen sadarwa.
Ko a watan Yulin da ya gabata, wasu gungun barayin mutane sun yi garkuwa da mutane goma sha biyar a garin Maradun, kamar yadda kaakakin majalisar dokokin jahar, Sunusi Rikiji ya bayyana ma manema labaru.
Fatanmu anan shine Allah ya bayyana wadannan tagwaye, Ya tseratar dasu da sauran wadanda ke hannun miyagun mutane a jahar Zamfara, Arewa da ma Najeriya gaba daya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng