2019: Takai ya bar PDP zai yi takarar Gwamna a Jam’iyyar PRP

2019: Takai ya bar PDP zai yi takarar Gwamna a Jam’iyyar PRP

Mun samu labari a jiya cewa daya daga cikin wadanda su ka nemi Gwamnan Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar PDP Malam Salihu Sagir Takai ya fice daga Jam’iyyar adawar ya koma Jam’iyyar PRP.

2019: Takai ya bar PDP zai yi takarar Gwamna a Jam’iyyar PRP
Malam Salihu Takai ya koma Jam’iyyar PRP a Kano
Asali: UGC

Salihu Takai wanda yana cikin manyan ‘Yan takarar Gwamna a Jihar Kano ya bar PDP ne a sakamakon tsaida Surukin tsohon Gwamnan Jihar Kano Abba Yusuf da aka yi a matsayin ‘Dan takarar Jam’iyyar a zaben 2019.

Wannan labari ya zo mana ne daga Shugaban masu masu taya Takai yakin neman Gwamna a kafafen yada labarai watau Muhammad Bashir Aminu. Takai ya nemi Gwamnan Jihar Kano a zaben 2011 da 2015 amma bai dace ba.

Mai neman Gwamnan dai ya dauki wannan mataki ne mako guda bayan an aikawa Hukumar zabe na kasa sunan ‘Yan takaran 2019 inda PDP ta sa sunan Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda zai rike mata tutan Gwamna a Kano.

KU KARANTA: Salihu Sagir Takai ba zai fasa neman takarar Gwamna ba a 2019

Kwanaki dai bangaren Sanata Umar El-Masud Doguwa na PDP tace Malam Salihu Sagir Takai ne ‘Dan takaran ta inda ta ke kalubalantar matakin da ‘Yan Kwankwasiyya wadanda su ka dawo Jam’iyyar PDP daga baya su ka dauka.

Sai dai Uwar Jam’iyyar ta PDP ba ta yi na’am da wannan mataki ba inda tayi watsi da sunan Malam Salihu Sagir Takai wanda tun lokacin aka fara rade-radin cewa babban ‘Dan siyasar zai bar Jam’iyyar sakamakon wannan mataki.

Abba Yusuf shi ne ya lashe zaben fitar da gwani a Jam'iyyar PDP. Zaben dai ya zo da ce-ce-ku-ce domin an yi sa ne a gidan tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda Surukin ‘Dan takaran ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng