Adadin kudin yakin neman zabe da dokar Najeriya ta amincewa 'yan takara kashewa
- A ranar Talata ne majalisar dattijai ta saka iyaka a kan adadin kudin da 'yan takarar kujerar shugaban kasa, gwamnoni da majalisar dattijai zasu kashe yayin yakin neman zabe
- Wannan doka wani bangare ce na dokar yiwa tsarin zabe kwaskwarima da shugaba Buhari ya ki sahalewa majalisar bayan ta gabatar da kudirin har sau uku
- Yanzu dai majalisar ta sake yiwa kudirin gyare-gyare da tankade da rairaya, sannan ta sake aika shi zuwa ga shugaba Buhari
A ranar Talata ne majalisar dattijai ta saka iyaka a kan adadin kudin da 'yan takarar kujerar shugaban kasa, gwamnoni da majalisar dattijai zasu kashe yayin yakin neman zabe. Kazalika majalisar ta saka iyaka a kan adadin da 'yan takarar kujerar majalisar wakilai, majalisar dokoki da shugabannin kananan hukumomi zasu kashe.
Wannan doka wani bangare ce na dokar yiwa tsarin zabe kwaskwarima da shugaba Buhari ya ki sahalewa majalisar bayan ta gabatar da kudirin har sau uku.
Wannan shine karo na hudu da majalisar ta dattijai ta sake aikewa da Buhari kudirin yiwa tsarin zabe kwaskwarima.

Asali: Depositphotos
Shugaba Buhari ya ki amincewa da bukatar majalisar ne saboda wadansu kunbiya-kunbiya a cikin kunshin kudirin da ya ce bai fahimta ba.
Yanzu dai majalisar ta sake yiwa kudirin gyare-gyare da tankade da rairaya, sannan ta sake aika shi zuwa ga shugaba Buhari.
DUBA WANNAN: An yiwa wasu gwamnonin APC zanga-zanga bisa zarginsu da yunkurin cin amanar Buhari
Daga cikin dokokin kudirin ne majalisar ta saka iyaka a kan adadin kudin da 'yan takarar kujeru daban-daban zasu kashe yayin yakin neman zabe.
A cikin sabuwar dokar, dan takarar shugaban kasa ba zai kashe kudin da su ka wuce biliyan N5b ba, dan takarar gwamna kuma biliyan N1bn. Mai neman kujerar Sanata an yi masa iyaka ta kashe miliyan N250m, dan takarar majalisar wakilai kuma miliyan N100m.
Naira miliyan N30m ne iyakar kudin da dan takarar majalisar dokoki da karamar hukuma zai kashe, Naira miliyan N5m kuma ga mai neman kujerar kansila.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng