EFCC ta kama dan takarar gwamna a Kano bisa laifin damfarar N100m

EFCC ta kama dan takarar gwamna a Kano bisa laifin damfarar N100m

Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da dan takarar gwamna a Kano karkashin jam'iyyar Green Party of Nigeria (GPN), Abdulkarim Abdulsalam a gaban kuliya.

An gurfanar da Abdulsalam ne tare da wani Ebere Nzechukwu a babban kotun tarayya da ke jihar Kano bisa zarginsu da zambar kudi sama da N100 miliyan.

Alkalin kotun, Lewis Allagoa ya bukaci hukumar yaki da rashawar ta gabatar da dukkan wadanda ake tuhuma sai dai lauyan mai shigar da kara, Johnson Ojogbane bai samu ikon gabatar da Abdulsalam a kotun ba.

EFCC ta kama dan takarar gwamna a Kano bisa laifin damfarar N100m
EFCC ta kama dan takarar gwamna a Kano bisa laifin damfarar N100m
Asali: Twitter

Sai dai ya gabatarwa kotun da Nzechukwu.

DUBA WANNAN: Wata mace ta yi karar mijinta a kotu bisa gazawarsa wajen biya mata hakin kwanciyar aure

Ojogbane ya yi ikirarin cewar Abdulsalam ya ki amsa gayyatar kotun hakan ya sa ya roki kotun da daga cigaba da sauraron karar domin ya samu ikon gabatar da sauran wadanda ake tuhumar.

A cewarsa, Abdulsalam da wani Michael Edosa sun hada baki a watan Augustan 2014 inda suka karbe miliyoyin naira daga wani Jamman Al-Azmi.

"Sun gabatar da kansu a wajen Al-Azmi a matsayin 'yan kasuwa da suyi hadin gwiwa da shi domin wata kasuwanci alhalin sun san karya su keyi," inji Ojogbane.

Ana tuhumarsu da aikata laifuka guda tare masu alaka da rashawa da zamba.

An dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel