Gwamnatin tarayya ta yi magana a kan bayyanar Nnamdi Kanu
- A yau, Talata, ne gwamnatin tarayya ta yi magana a kan bayyanar Nnamdi Kanu, shugaban 'yan aware ta kabilar Igbo (Biyafra) bayan an bayyana cewar ya bace
- Tun watan Satumba na shekarar 2017 ba a kara gani ko jin duriyar Nnamdi Kanu ba
- A wani sako da ya fitar ta haramtaccen gidan Radiyonsa na Biyafra, Kanu ya tabbatar da cewar yana kasar Isra'ila
A yau, Talata, ne gwamnatin tarayya ta yi magana a kan bayyanar Nnamdi Kanu, shugaban 'yan aware ta kabilar Igbo (Biyafra) bayan an bayyana cewar ya bace
Tun watan Satumba na shekarar 2017 ba a kara gani ko jin duriyar Nnamdi Kanu ba.
A watan na Satumba ne 'yan kabilar Igbo su ka yi zargin cewar dakarun sojin Najeriya sun kashe Kanu da iyayensa bayan sun kai wani samame gidansa.

Asali: Facebook
Sai dai a wani yanayi mai abun mamaki, sai ga shi an hango Kanu ranar Lahadin da ta gabata a kasar Isra'ila yana bauta a bangon tarihi dake garin Jerusalem.
A wani sako da ya fitar ta haramtaccen gidan Radiyonsa na Biyafra, Kanu ya tabbatar da cewar yana kasar Isra'ila.
Da yake magana a kan bayyanar Kanu, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewar: "idan har da gaske bidiyon da ake nunawa gaskiya ne, gaskiya ta bayyana cewar gwamnatin tarayya ba ta kashe Kanu ba kamar yadda wasu ke zargi."
DUBA WANNAN: Shugaban kasar Kamaru mai shekaru 85 ya sake lashe zabe a karo na 7
Shehu ya yi waiwaye a kan yadda su ka fuskanci matsin lamba a kan zargin cewar sun sa an kashe Kanu ko kuma sace shi.
"Har fadar majalisar dinkin duniya sai da 'yan kungiyar IPOB su ka kai korafin cewar gwamnatin tarayya ta sa an sace Kanu kafin daga baya ma su zarge mu da hallaka shi," a cewar Shehu.
A maganar da ya yi ranar Lahadi Kanu ya ce zai dawo Najeriya tare da yin kira ga magoya bayansa da su kauracewa zaben shekarar 2019 mai zuwa.
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng