Wani Mummunan Hatsari ya salwantar da rayuwar wata Mahaifiya da Jariran ta 2 a jihar Akwa Ibom

Wani Mummunan Hatsari ya salwantar da rayuwar wata Mahaifiya da Jariran ta 2 a jihar Akwa Ibom

Wata Mahaifiya da jariran ta biyu masu shekarun 2 da 3 na cikin rayukan Mutane 6 da suka salwanta a ranar Asabar din da ta gabata a sanadiyar wani mummunan hatsari da ya auku a jihar Akwa Ibom dake Kudancin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, Motocin hayar biyu kirar Bus da kuma Tasi sun gwabzawa juna a babbar hanyar Afahaobong dake yankin Ikot Ese na karamar hukumar Etim Ekpo a birnin na Uyo.

Masu batar da agajin lafiya ta gaggawa da suka kai dauki kan wannan fasinjoji 9 da hatsarin ya ritsa da su sun tabbatar da salwantar rayukan Mutane 6 nan take.

Kakakin hukumar kula da manyan hanyoyi ta FRSC, Mista Justice Agwu, shine ya tabbatar da wannan mummunan lamari a jiya Litinin.

Wani Mummunan Hatsari ya salwantar da rayuwar wata Mahaifiya da Jariran ta 2 a jihar Akwa Ibom
Wani Mummunan Hatsari ya salwantar da rayuwar wata Mahaifiya da Jariran ta 2 a jihar Akwa Ibom
Asali: Depositphotos

Mista Agwu ya bayyana takaicin sa dangane da yadda aukuwar hatsari a jihar Akwa Ibom ta yi kamari da ya nemi a fadakar da al'umma a wuraren taro musamman wurin ibada da kuma makarantu domin saukaka wannan annoba.

KARANTA KUMA: Zanga-Zangar goyon bayan Oshiomhole ta barke a ofishin jam'iyyar APC

Ya kuma nemi dukkanin hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki akan tabbatar da kiyaye dokokin hanya da kuma tsawatarwa a kan guje-guje da suka sabawa ka'ida.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Najeriya da wasu kasashe uku na nahiyyar Afirka za su karbi bakuncin wani babban bako daga kasar Amurka, Mista Tibor Nagy, Mataimakin sakataren harkokin nahiyyar Afirka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel