Rikici: An shiga takun saka tsakanin Dankwambo da shugaban jam'iyyar PDP a Gombe

Rikici: An shiga takun saka tsakanin Dankwambo da shugaban jam'iyyar PDP a Gombe

- Rigima ta barke tsakanin Dankwambo da ciyaman din jam'iyyar PDP na Gombe kan zabin dan takarar majalisa

- Wannan ya biyo bayan an canja sunan na hannun daman gwamnan da ya lashe zaben cikin gida na yankin Billiri ta Gabas da sunan tsohuwar kwamishinan mata na jihar

Wata sabuwar rikici ta kunno kai a jam'iyyar PDP reshen jihar Gombe wadda ka iya raba kawunnan 'yan jam'iyyar saboda canja sakamakon zaben fidda gwani da a kayi a mazabar Billiri ta Gabas da ke Jihar.

Rikicin ya janyo gwamna jihar Ibrahim Hassan Dankwambo ya raba jihar the ciyaman din jam'iyyar na jihar Joel Adamu Jafaga kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Rikici: An shiga takun saka tsakanin Dankwambo da shugaban jam'iyyar PDP
Rikici: An shiga takun saka tsakanin Dankwambo da shugaban jam'iyyar PDP
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Masoyin Atiku da ya tuka keke daga Owerri zuwa Abuja ya kare a gadon asibiti

Rikicin dai ya samo asali ne sakamakon canja sunan na hannun daman gwamna, Honarabul Rambi Ibrahim Ayala wanda ya lashe zaben cikin gida a jihar da sunan tsohuwar Kwamishiniyar Harkokin Mata da Jin Dadin Al'umma, Mrs Rabi Daniel da jam'iyyar tayi.

A yayin da ya ke jawabi ga yan jarida a makon da ta gabata, Rambi Ayala ya bayyana cewar shine ya yi nasara a zaben inda ya samu kuri'u 25 cikin 49 da aka tantance kuma jami'in zabe, Barr J.A. Lawal ya sanar da sunarsa a matsayin wanda ya yi nasara a zaben a idanun jami'an INEC, 'yan jarida da hukumomin tsaro.

"Sai dai murna ta ta koma ciki a ranar Alhamis yayin da na gano cewar wasu 'yan takarar suna cike fom E.C 4B (iii) da aka kawo daga Abuja amma ta na tuntubi sakataren jam'iyyar, Alhaji Bba Sani domin ya bani nawa sai ya ce jam'iyyar ta maye gurbin suna na da na Rabi Daniel," inji Ayala.

Daga karshe Ayala ya yi kira ga mogoya bayansa su kwantar da hankulansu inda ya ce zai bi hanyoyin da doka ta tanada domin bin kadin hakkinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel