Atiku ya kira ministan Buhari 'yariman sheka karya na APC"

Atiku ya kira ministan Buhari 'yariman sheka karya na APC"

Kwamitin yakin neman zaben Atiku (APCO) ya bayyana ministan yada labarai da al'adu na gwamnatin tarayya, Alhaji Lai Mohammed, a matsayin shugaban shimfida karya na makaryatan jam'iyyar APC.

Kwamitin na wannan kalamai ne a matsayin raddi ga wani rahoto da kafafen yada labarai su ka rawaito Lai Mohammed na cewar kafafen yada labarai na duniya ba su gamsu da tsaftar dukiyar Atiku ba.

Mohammed, yayin gabatar da wata lakca a gidan Chatham da ke kasar Ingila, ya bayyana cewar gwamnatinsu ta cika dukkan alkawuran da ta dauka kafin zaben shekarar 2015.

Atiku ya kira ministan Buhari 'yariman sheka karya na APC"
Atiku da Lai Mohammed
Asali: Depositphotos

Sai dai a jawabin da APCO ta fitar, ta bayyana cewar tun bayan nasarar Atiku a zaben fidda 'yan takara na PDP kafafen yada labarai na duniya ke yabonsa.

DUBA WANNAN: An kama mutane 22 da ke da hannu a rikicin Kaduna

Kazalika kwamitin yakin neman zaben na Atiku ya soki kalaman Mohammed na cewar sun cika dukkan alkawuran da su ka dauka tare da mayar ma sa da martanin cewar gwamnatinsu ta kara haddasa fatara da talauci ne kawai a tsakanin 'yan Najeriya.

APCO ta bayyana cewar idon 'yan Najeriya yanzu ya bude, a saboda haka babu wata farfaganda da za ta saka su sake zaben APC a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel