Allah ya kare masifa: Tankar dakon man fetur ta fado daga gadar Odetola a Legas

Allah ya kare masifa: Tankar dakon man fetur ta fado daga gadar Odetola a Legas

- Tankar dakon man fetur da ke makare da dizel ta fado daga kan gadar Otedola a yayin da take tafiya zuwa Berger a garin Legas

- Tankar ta fado ne da yammacin yau, Litinin, kuma tuni jami'an bayar da agajin gaggawa sun isa wurin domin kiyaye afkuwar hatsari

- Labarin faduwar tankar ya fito ne daga shafin hukumar kula da tabbatar da bin dokokin tuki ta jihar Legas (LASTMA) na Tuwita

Wata tankar dakon man fetur da ke dauke da dizel ta fado daga kan gadar Otedola a yayin da take tafiya zuwa Berger a garin Legas.

Tankar ta fado ne da yammacin yau, Litinin, kuma tuni jami'an bayar da agajin gaggawa sun isa wurin.

An datse hanyar, duk da ababen hawa na ratsewa su wuce ta gefen tankar.

Allah ya kare masifa: Tankar dakon man fetur ta fado daga gadar Odetola a Legas
Tankar dakon man fetur ta fado daga gadar Odetola a Legas
Asali: Twitter

Allah ya kare masifa: Tankar dakon man fetur ta fado daga gadar Odetola a Legas
Tankar dakon man fetur ta fado daga gadar Odetola a Legas
Asali: Twitter

Labarin faduwar tankar ya fito ne daga shafin hukumar kula da tabbatar da bin dokokin tuki ta jihar Legas (LASTMA) na Tuwita: "Tankar dakon mai ta fado daga gadar Odetola, jami'an agaji sun isa wurin. Ana shawarar masu ababen hawa su kauracewa hanyar," kamar yadda ya ke a sakon da LASTMA ta saki.

DUBA WANNAN: Rikicin Kaduna: El-Rufa'i ya zagaya sassan da rikici ya shafa, ya ziyarci asibitoci (Hotuna)

Sannan su ka kara fitar da wani sakon da ke cewa, "Tankar makare ta ke da dizel. Dukkan jami'an mu na sashen bayar da agajin gaggawa na wurin. Mun rufe hanyar domin tabbatar da ba a samu afkuwar hatsari ba. Muna bawa ma su ababen hawa hakuri bisa rufe hanyar tare da shawartar su su yi amfani da wasu hanyoyin domin isa inda za su.

"Tankar ta fadi ne a gadar Otedola, daidai Mobil INW, a hanyar zuwa Berger.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel