Rashawa ta yiwa Najeriya Katanga da ci gaba - Sani Lulu

Rashawa ta yiwa Najeriya Katanga da ci gaba - Sani Lulu

Mun samu cewa tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Alhaji Sani Lulu Abdullahi, ya bayyana rashawa a matsayin wani jigo kuma babban kalubale na katutu da ya zamto cikas ga ci gaban kasar nan ta Najeriya.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ta ruwaito, Sani Lulu ya bayyana cewa ba bu wani garkuwa da riga kafin wannan babban kalubale da kasar nan ta ke fusakanta a halin yanzu da ya wuce jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban hukumar ya bayyana hakan ne yayin nadinsa a matsayin jagoran kungiyar Mata magoya bayan shugaba Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, inda ya jaddada tsayuwar dakansa akan tabbatar da nasarar shugaba Buhari a karo na biyu.

Rashawa ta yiwa Najeriya Katanga da ci gaba - Sani Lulu
Rashawa ta yiwa Najeriya Katanga da ci gaba - Sani Lulu
Asali: UGC

A yayin bayyana shugaba Buhari a matsayin tabarraki ga kasar nan, Sani Lulu ya kuma ya yabawa kwazon shugaban kasar dangane da jajircewar sa akan tsarkake annobar cin hanci da rashawa da ta zamto katutu da kuma cikas na ci gabanta.

KARANTA KUMA: Wani dan Shekara 38 ya yiwa 'yar shekara 6 fyade a jihar Ogun

Kazalika Sani Lulu ya kuma yabawa kwazon shugaba Buhari dangane da jajircewar sa akan harkokin tsaro musamman ta'addancin kungiyar Boko Haram.

Tsohon shugaban hukumar wasannin ya bayyana cewa, kwazon shugaba Buhari akan harkokin tsaro ya nakasta ta'ddancin Boko Haram wanda da tuni ta mamaye kaso mai tsoka na kasar nan musamman Arewacin Najeriya.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, ta bayar da tabbacin adadin al'ummar Najeriya da za su yi zabe a 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng