2019: Kwankwaso ba zai nemi kujerar Sanatan Kano ta tsakiya ba
Mun samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso yayi watsi da tayin takarar kujeran da yake kai da aka yi masa ganin ya fadi zaben takarar Shugaban kasa a karkashin PDP.

Asali: UGC
Jam’iyyar adawa ta PDP da ‘Dan takarar da aka tsaida na Sanatan Kano ta tsakiya ta tuntubi tsohon Gwamnan ko zai yi kokarin zarcewa a kan kujerar sa. Sanata Rabiu Musa Kwankwaso dai ya nuna sha’awar bai da bukatar kujerar.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana cikin wadanda su ka rasa takarar kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP a zaben da aka yi inda Atiku Abubakar yayi nasara. Yanzu dai ana ganin cewa ‘Dan siyasan ya tashi biyu-babu a PDP.
KU KARANTA: Abin da ya sa na kinkimo Ganduje ya zama Gwamna - Kwankwaso
Sauran ‘Yan takaran Shugaban kasa irin su Bukola Saraki da Rt. Hon. Aminu Tambuwal tuni su ka koma neman takaran kujerun da su ke rike da su. Sai dai Sanatan na Kano ta tsakiya ya nuna cewa bai sha’awar aikin Majalisa bayan 2019.
Yanzu haka dai ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Dala a Majalisar Wakilai ta Tarayya Hon. Aliyu Madakin Gini shi ne zai nemi takaran kujerar Sanatan wanda Kwankwaso ya ke kai a 2019 inda zai kara da Malam Ibrahim Shekarau a APC.
Dazu kun ji cewa har yanzu rikicin Jam’iyyar PDP a Jihar Kano bai kare ba bayan da wani ‘Dan takaran Gwamna ya nemi Kotu ta dakatar da Surukin Rabiu Kwankwaso watau Abba Yusuf daga zaben 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng