Cikin masu bin gwamnati bashi a Nigeria Airways 900 tuni sun mutu basu ci fanshonsu ba
- Bincike ya nuna cewa mutane 900 sun rasu a cikin wadanda sukayi ritaya daga aikin tukin jirgi
- Wasu daga cikin su kuma suna cikin matsanancin hali
- Binciken ya tabbatar da cewa mutanen tsofaffin ma'aikatan hukumar jiragen sama ta Nageriya ne

Asali: Depositphotos
Shu'aibu Alfa shugaban kwamitin da aka kafa akan bincike tsofaffin ma'aikatan hukumar tukin jirgi ta Nageriya don biyansu hakkunan su tun daga shekara 2004 har zuwa yanzu yace mutane 900 daga cikin su sun rasu.
Alfa ya bayyana haka ne a tattaunawar da yayi da NAN a Kano ranar Juma'a.
Akwai ragowar santoci guda Uku da basu karasa gudanar da nasu binciken Ba.
Yace a tsayin shekaru 15 mutane 900 sun rasu wasu kuma lafiya tayi karanci a garesu yayinda wasu kuma suke fuskantar tsananin rayuwa.
DUBA WANNAN: Dubi yawan wutar lantarki da za'a samu kuma a 2019
Binciken ya tabbatar mana da cewa mutanen tsofaffin ma'aikatan hukumar tukin jirgi ta Nageriya ne .
Mun kafa wata kungiya da zata fara biyansu hakkunan su.
A cikin kungiyar akwai mutane daga hukumar EFCC, ICPC, PITAD.
Sannan ya nemi goyan bayan shuwagabannin gargaji da na addini da kuma yan siyasa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng