Hukumar NIA tayi gargadi kan wani Magani mai dauke da Tsokar 'Dan Adam da zai shigo Najeriya daga Kasar China
Mun samun rahoton cewa za a shigo da wata kwayar magani mai dauke da tsoka da kuma sassan jiki na bil Adama zuwa Najeriya daga kasar China.
Hukumar leken asirin ta NIA, National Intelligence Agency, ta gargadi dukkanin hukumomin tsaro musamman hukumar hana fasakauri ta Kastam, akan su sanya idanun lura dangane da wannan kwaya 'yar kasar China mai dauke da sassan jikin bil Adama.
Binciken manema labarai na jaridar Nigerian Tribune ya tabbatar da cewa, wannan kwayar magani na dauke da garin tsoka ta sassan jikin bil Adama da aka hada ta da gawar Matattun Jarirai.

Asali: Depositphotos
Rahotanni sun bayyana cewa, an hada wannan kwayoyi na magunguna a Arewa maso Gabashin kasar China daga sassan jikin jarirai da aka gididdiba gunduwa-gunduwa kana aka soye su kurmus kuma aka dake su ka zama gari.
Kamar yadda jaridar ta Nigerian Tribune ta ruwaito, hukumar hana fasakauri ta kasar Koriya ta Kudu ta datse dubunnan wannan miyagun kwayoyi a shekarar 2012 da ta gabata.
KARANTA KUMA: Matsalolin Wutar Lantarki ba za su gyaru da Siddabaru ba - Fashola
Kwararrun masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, wannan kwaya tana da nasaba da cutar hanta da a turance ake ce da ita Hepatitis B Virus.
A sanadiyar wannan lamari hukumar NIA ta Najeriya ta gargadi dukkanin hukumomin tsaro da na lafiya ma su ruwa da tsaki akan su sanya idanun lura kan wannan mummunar barazana mai kunshe da cin zarafi da wulakantas da 'Dan Adam.
A yayin haka jaridar LEGIT.ng ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i, ya samu jinjina daga babban bankin duniya dangane da kwazon sa na rage sarkakiyar dake cikin harkokin kasuwanci a jihar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng