Saboda yadda Jonathan ya sallama mani mulki ya sa nake kallon sa da mutunci – Buhari
- Shugaba Muhammadu Buhari ya kara jinjinawa Jonathan na amincewa da zaben da aka yi a 2015
- Shugaban kasar yace a sakamakon hakan ne yake kallon tsohon Shugaban na Najeriya da girma
- Buhari ya kuma nemi ‘Yan wasan kwaikwayon su yi kokari wajen kawo zaman lafiya a Najeriya

Asali: Twitter
A jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi dalilin da ya sa yake rike tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan da girma da arziki. Buhari ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da ‘Yan wasan kwaikwayon Hausa.
Muhammadu Buhari ya kara yabawa matakin da tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya dauka a 2019 bayan ya sha kayi a zabe. Wannan abu tilo ne ya sa Shugaba Buhari yake kallon Jonathan da idanun girma da martaba.
KU KARANTA: Idan Buhari yayi sake Atiku na iya mamayan sa a 2019
Buhari yace Jonathan yayi Mataimakin Gwamna, ya kuma yi Gwamna daga baya a Jihar Bayelsa, har ta kai yayi Mataimakin Shugaban kasa kafin ya samu mulkin Najeriya gaba daya, amma duk da wannan ya mika mulki cikin ruwan-sanyi.
Wannan abu da Goodluck Jonathan yayi a 2015 ne ya sa Buhari yake kara jinjina masa. Gwamnan Jihar Kaduna Nasir el-Rufai da Gwamna Simon Lalong su na cikin wadanda su ka halarci taron da aka yi a cikin fadar Shugaban kasa a Abuja.
‘Yan wasan kwaikwayon na Kannywood dai sun nuna cewa za su marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma duk sauran ‘Yan takaran Jam’iyyar APC mai mulki baya a zaben da za ayi a 2019.
Asali: Legit.ng