Shugaba Buhari na ganawa da shugabannin tsaro na Kasa
Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu cewa, a yanzu yanzunan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kebance da shugabannin tsaro na kasa inda suke gudanar da wata muhimmiyar ganawa a fadarsa ta Villa dake babban birnin kasar nan na Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan ganawa ta fara gudana ne jim kadan bayan zaman majalisar tattalin arziki na kasa da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Ganawar ta na ci gaba da gudana a halin yanzu bayan kwanaki kadan da 'yan ta'adda na Boko Haram suka yiwa wata ma'aikaciyar agaji, Hauwa Liman kisan mummuke a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Asali: UGC
Mambobin majalisar tsaro dake halartar taron a fadar ta shugaban kasa sun hadar da; babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Babagana Monguno; Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali; Shugaban dakarun soji na kasa, Janar Gabriel Olanisakin; Shugaban hafsin sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai da kuma shugaban hafsin sojin ruwa; Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas.
KARANTA KUMA: Jam'iyyu 17 sun gabatar da jerin Sunayen 'yan takarar Shugaban Kasa da Majalisar tarayya
Saurna jiga-jigan na tsaro sun hadar da; Shugaban hafsin sojin sama, Air Mashal Abubakar Sadique; shugaban hukumar NIA, Ahmed Abubakar; Sufeto Janar na 'yan sanda; Ibrahim Idris da kuma shugaban hukumar tsaro ta DSS, Yusuf Magaji Bichi.
Jaridar LEGIT.ng ta kuma ruwaiito cewa, tsohon Ministan sadarwa Cif Tony Momoh, ya bayyana cewar rawar da shugaba Buhari ya taka a kan karagar mulki ta kasar nan za ta yi tasirin gaske wajen samun nasara ta lashe babban zabe na 2019.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng