Tsohon shugaban kasar Sudan, Al-Dahab ya rasu a Saudiyya
- Tsohon shugaban kasar mulkin soja na Sudan, Abdulrahman Al-Dahab ya rasu
- Al-Dahab ya rasu ne a babban birnin kasar Saudiya wato Riyadh
- Abdulrahman Al-Dahab ya rasu yana da shekaru 83 da duniya

Asali: Twitter
Tsohon shugaban kasar Sudan Abdulrahman Al-Dahab ya rasu a Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya kamar yadda wani gidan talabijin na kasar, Al Arabiya ya ruwaito a jiya Alhamis.
DUBA WANNAN: Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana matsayar ta kan batun karin albashi
Sai dai tashar talabijin din ba ta bayar da cikaken bayanin musababbin rasuwar na Al-Dahab ba. Al-Dahab shine shugaban kasa na biyar a tarihin Sudan kuma ya rasu ne yana da shekaru 83 a duniya.
Al-Dahab wanda tsohon soja ne ya mulki kasar daga ranar 6 ga watan Afrilun 185 zuwa 6 ga watan Mayun 1986 bayan ya yi juyin mulki a wancan lokacin inda ya hambarar da Nimeiry daga karagar mulki.
Tsohon shugaban kasar ya zaman Ciyaman din Gwamnatin mulkin soji a kasar har zuwa shekarar 1986 da aka gudanar da zabe sannan ya mika mulki ga Sadiq al-Mahdi kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito.
Asali: Legit.ng