Jama’a ayi hattara: Ba na bada tallafin naira dubu goma goma – Atiku

Jama’a ayi hattara: Ba na bada tallafin naira dubu goma goma – Atiku

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya nesanta kansa da wasu tsarin tallafi dake yawo a kafafen sadarwar wanda ake cewa shine ya hidimar tallafa ma jama’a da jarin naira dubu goma goma.

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito Atikun ya bayyana haka ta bakin kungiyar yakin neman zabensa, inda cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis a garin Abuja ta bayyana cewa babu hannun Atiku ko na kungiyar yakin neman zabensa a cikin wannan lamari.

KU KARANTA: Abin nema ya samu: Kotu ta baiwa EFCC izinin rike Fayose na tsawon kwanaki 14

Jama’a ayi hattara: Ba na bada tallafin naira dubu goma goma – Atiku
Atiku
Source: Twitter

“Mun samu rahoton wani tsarin tallafi mai taken ‘Atiku Disbursement Program’ dake kira ga jama’a dasu bada wani adadi na kudi, wanda zasu ninka musu a matsayin tallafi ne daga Atiku Abubakar, bamu da hannu a cikin wannan lamari, da ire irensa.

“Kuma mun shaida ma jama’a cewa sahihan hanyoyin kafafen sadarwar Atiku Abubakar na zamani sune;

www.atiku.org (Blog)

www.facebook.com/atiku.org (Facebook)

www.twitter.com/atiku (Twitter)

www.instagram.com/aatiku (Instagram)”

Daga karshe sanarwar ta yi kira ga jama’a dasu yi watsi da duk wata sanarwar da ake ikirari daga ofishin Atiku Abubakar suka fito, matukar ba daga kafafen sadarwar nan na zamani suka fito ba.

daga haka kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2019 ta bukaci jama’a da kada su kuskura su fada wannan tarko nay an damfara, yan damfarar dake kokarin sun bata ma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku suna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng