Zaben shugaban kasa: Bamu da yar mowa ko yar bora a Najeriya – Amurka

Zaben shugaban kasa: Bamu da yar mowa ko yar bora a Najeriya – Amurka

Gwamnatin kasar Amurka ta bayyana cewa bata da wani dan takarar da take mara ma baya a babban zaben shekarar 2019 dake karatowa, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana.

Majiyar Legit.com ta ruwaito wani jami’I a ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya, Phillip Franz ne ya bayyana haka a yayin da yake ganawa da manema labaru a jahar Katsina, inda ya kai ma gwamnan jahar Aminu Bello Masari ziyara.

KU KARANTA: Cacar baki tare da nuna ma juna yatsa ya kaure tsakanin Dino Melaye da Akpabio

Jim kadan bayan ganawarsa da gwamnan jahar Katsina ne Mista Franz ya bayyana ma yan jaridu cewa kasar Amurka ba ta da wan dan takara da ta ware da nufin zata bashi goyon baya, haka nan bata da wani dan takara da take ki.

Sai dai Franz yace bukatar gwamnatin kasar Amurka kawai shine ganin an gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaben a shekarar 2019.

“Ina jaddada cewa kasar Amurka ba ta da wani dan takara a wannan zabe, dan takararmu kawai shine tsarin gudanar da zaben, muna girmama ikon Najeriya na tafiyar da kanta da kanta ba tare da an sanya mata baki a harkokinta ba.” Inji Franz.

Jami’in jakadancin ya kara da tabbatar ma manema labarum cewa gwamnatin Amurka za ta bada gudunmuwa daidaida gwargwado don ganin an inganta zaben 2019, ta hanyar taimakawa wajen shirya zaben gaskiya da gaskiya.

“Muna goyon bayan zaben gaskiya da gaskiya, kuma a shirye muke mu bada gudunmuwa don ganin an shirya irin wannan sahihin zabe, wanda mafi rinjayen al’umma da masu sa ido zasu gamsu da ingancinsa.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wata babbar kotun tarayya ta haramta ma jam’iyyar APC reshen jahar Delta mika ma hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, sunayen yan takararta a jahar, hakanan ma ta haramta ma INEC amsan sunayen har sai ta yanke hukunci akan wata kara da yayan APC suka shigar gabanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng