'Dan Majalisar APC ya sauya sheka zuwa PDP a jihar Sakkwato

'Dan Majalisar APC ya sauya sheka zuwa PDP a jihar Sakkwato

Mun samu cewa wani dan majalisar dokoki ta jihar Sakkwato, Alhaji Muhammad Bashir, wanda ya rasa samun tikitin jam'iyyar APC na takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya ya sauya shekarsa zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Alhaji Bashir ya bayyana hakan ne a farfajiyar majalisar dokoki ta jihar a jiya Laraba. Ya ke cewa a halin yanzu duk wata biyayya da mubaya'arsa ta sauya sheka zuwa ga jam'iyyar PDP.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, dan majalisar ya sha kashin tsiya yayin neman tikitin takarar kujerar majalisa wakilai na mazabar Yabo/Shagari a hannun Alhaji Abubakar Yabo yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da aka gudanar a Birnin Shehu.

Gwamnan jihar Sakkwato; Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan jihar Sakkwato; Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

Jaridar LEGIT.ng ta fahimci cewa, Alhaji Bashir ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP bisa tanadin sashe na 109 cikin kundin tsarin mulkin Najeriya da ya bayar da dama ta kwarar romon Dimokuradiyya.

KARANTA KUMA: Tazarcen Buhari zai bude kofa ga 'Yan Kabilar Ibo ta cin Gajiyar kujerar a 2023

A yayin mayar da martani dangane da wannan lamari, wani dan majalisa na jam'iyyar APC mai wakilcin karamar hukumar Gudu, Alhaji Sani Yakubu, ya bayyana cewa babu wani ban mamaki kan sauyin shekar Alhaji Bashir domin kuwa ya dade yana rara gefe a cikin jam'iyyarsu.

Kazalika jaridar LEGIT.ng ta ruwaito cewa, wani Matashi da ya gawurta wajen aikata Luwadi, Adamu Muhammad, bayan shiga hannun hukuma a jihar Neja ya yi baja kolin dalilin sa na neman maza musamman kananan Yara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel