Bullar hoton Atiku da Trump - An gano gaskiyar maganar

Bullar hoton Atiku da Trump - An gano gaskiyar maganar

A yayin da ya rage saura watanni hudu a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, yakin neman zabe tsananin manyan 'yan takara, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da shugaba Buhari na jam'iyyar APC, na kara zafi.

Tun bayan tabbatar da Atiku a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP, masu sukar sa su ke kalubalantar shi da ya ziyarci kasar Amurka idan ya isa.

A yayin da ake cigaba da gorantawa Atiku a kan gazawar sa ta ziyartar Amurka bisa tsoron hukumomi a kasar za su kama shi, sai ga shi wani hoto da ke nuna Atiku da shugaba Trump na kasar Amurka ya bulla a dandalin sada zumunta.

Bullar hoton Atiku da Trump - An gano gaskiyar maganar
Hoton gaske: Buhari da Trump
Asali: Twitter

Bullar hoton Atiku da Trump - An gano gaskiyar maganar
Hoton Atiku da Trump na bogi
Asali: Twitter

Wani masoyin Atiku ne ya fara saka hoto a shafinsa na Facebook tare da bayanin cewar, "yanzu haka Atiku ya na kasar Amurka, duk ma su cewa ba zai iya ziyartar kasar Amurka ba sai su boye fuskar su saboda kunya."

DUBA WANNAN: Atiku ya bayar da tallafin miliyan N10m ga wasu jama'a da iftila'i ya afkawa

Sai dai wani bincike da da wani masanin anfani da yanar gizo, Jude Nwabuoke, ya gudanar ya gano cewar hoton na bogi ne.

Sannan ya kara da cewar, hasali ma hoton na shugaba Buhari ne da ya dauka da Trump a watan Afrilu amma sai aka yanke inda Buhari ya fito aka jona hoton Atiku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel