Karka biye wa ta jama'a kan nadin Justice Uwani Abba-Aji zuwa kotun qoli - Alkalan Najeriya ga Buhari
- Kungiyar shari'a ta kasa ta hori Shugaba Muhammadu Buhari da yayi biris da yan adawa akan zabar mai shari'ar kotun dauka, Uwani Abba-Aji zuwa kotun koli
- Wata kungiya mai suna Civic Society Network Against Corruption ta hori Shugaba Muhammadu Buhari da kada ya kai sunan mai shari'a Abba-Aji gaban majalisar ko kuma zata kalubalance shi a gaban kuliya
- NJC tace babu wani zargin rashawa akan mai shari'a Abba-Aji da zai sa CSNAC ta kalubalanci shugaban kasar
Wata kungiya, Civic Society Network Against Corruption CSNAC ta hori Shugaba Muhammadu Buhari da kada ya fara kai sunan mai shari'a Abba-Aji gaban majalisar dattawa don tabbatarwa ko kuma zata kalubalance shi a gaban kuliya.
Kungiyar shari'a ta kasa (NJC) ta hori shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi biris da yan adawa akan zaben mai shari'ar kotun daukaka kara Uwani Abba-Aji, akan daukaka ta zuwa kotun koli.
NJC ta bakin daraktan yada labarai, Soji Oye, a ranar laraba, tace babu wani zargin rashawa akan mai shari'ar da zai kawo adawar CSNAC.
DUBA WANNAN: An bada lasisin tace mai kafin Dangote ya kawo babbar
"Kungiyar ta dogara ne da cewa wata jaridar yanar gizo ta wallafa sunan mai shari'a Abba-Aji a ranar 16 ga watan Octoba, 2016,a cikin masu shari'ar da cibiyoyin tsaro ke bincika akan rashawa da cin hanci daga wani babban lauya dake fuskantar shari'a a gaban kotu. Kungiyar ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dakata da kai sunan Mista Abba-Aji ga majalisar dattawa har sai an wanke shi daga zargin rashawa."
Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng