Fusattatun 'yan gudun hijira sun farma tubabbun 'yan Boko Haram a Borno
- Tubabbun mayakan Boko Haram sun kusa haduwa da ajalinsu a sansanin 'yan gudun hijira da ke Maiduguri
- Hakan ya faru ne bayan wasu 'yan gudun hijira da ke sansanin sun gane fuskokinsu a matsayin wadanda suka kashe musu 'yan uwa a baya
- Rahotanni sun ce an kawo tubabbun 'yan Boko Haram din zuwa Maiduguri ne bayan sun kwashe watanni a wata sansanin da ke Gombe
Tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram 51 da ke sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi da ke Maiduguri suka tsira da rayyukansu da kyar bayan fusatattun 'yan gudun hijira da mayakan suka kashewa yan uwa sun harzaka domin daukan fansa kansu ranar Asabar da ta gabata.

Asali: Depositphotos
Daily Trust ta ruwaito cewar an fara kai tubabbun mayakan Boko Haram dun zuwa sansanin gudun hijira ne Bulumkutu ne da ke Maiduguri bayan sun kwashe wattani ana duba lafiyan kwakwalensu a sansanin yan gudun hijira d ake jihar Gombe karkashin shirin gwamnati na Operation Safe Corridor amma daga baya aka kai su sansanin gudun hijira da ke Gwoza.
DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama wasu matasa maza da mata 14 suna tika rawa zigidir a jihar Kebbi
Da isar su sansanin gudun hijrar ta Bakassi da ke Gwoza ne wasu da ke sansanin suka fara gane fuskokinsu a matsayin wadanda suka kashe musu iyaye, mata, mazaje da sauran 'yan uwa wadda hakan yasa suka yanke hukuncin daukan fansa kansu.
"Yan gudun hijiran sun farwa tubabbun 'yan Boko Haram din da suke zargin su ne suka kashe musu 'yan uwa da niyyar su dauki fansa a ranar Litinin da ta gabata," kamar yadda majiyar NAIJcom ta ruwaito.
Operation Lafiya Dole da sauran jami'an tsaro da ke yankin ba su yi tsokaci kan lamarin ba a lokacin rubuta wannan rahoton wani jami'in tsaro na sa kai 'Civilian JTF' ya bayyana cewar lamarin abin tsoro ne.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng