Dakarun soji sun ceto mata 7 da yara 5 daga hannun 'yan Boko Haram, hotuna
A yau, Litinin, 15 ga watan Oktoba, ne dakarun soji runduna ta 121 da hadin gwuiwar 'yan aikin sa kai na "civilian JTF" su ka yi nasarar ceto wasu mutane 15 daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.
Dakarun sun ceto mutanen ne yayin wani atisayen kakkabe ragowar mayakan kungiyar ta Boko Haram a yankin Bama da Pulka a jihar Borno.
Yayin atisayen, dakarun sojin sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram 2 tare da kwato wasu makamai da su ka hada da wasu bindigun baushe 2 da wata akwatun kayan aikin bayar da agajin gaggawa.
Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ya yabawa kokarin sojojin tare da basu umarnin cigaba da farautar mayakan kungiyar a duk inda su ke a fadin jihar Borno.
DUBA WANNAN: 2019: Kungiyar Dariqa ta bayyana dan takarar shugaban kasa da za ta zaba
A wani labarin mai alaka da wannan, juma'a, a ranar juma'a 12 ga watan Oktoba, ne da misalin karfe 5 na yamma, mayakan kungiyar Boko Haram suka kaiwa dakarun sojin Najeriya, runduna ta 118 harin bazata.
A sanarwar da hukumar sojin ta fitar a shafinta na Tuwita, ta bayyana cewar mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kai harin ne a sansanin sojojin da ke Arege a karamar hukumar Mobarr dake jihar Borno.
Sai dai jaruman dakarun sojin sun yi nasarar dakile harin tare da mayar da kaikayi kan mashekiya. Bayan sojojin sun dakile harin, sun yi nasarar kwace wasu makamai daga wurin 'yan ta'addar da su ka hada da wata motar dakon bindiga tare da lalata wasu motocin biyu. Yanzu haka dakarun sojin na cigaba da farautar mayakan kungiyar Boko Haram da su ka tsere bayan kai harin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng