An kusa bawa hammata iska tsakanin kakakin Buhari da na Atiku
Da safiyar yau, Litinin ne, aka yi wata mahawara mai zafin gaske tsakanin kakakin kwamitin kamfen din Buhari, Festus Keyamo, da na kwamitin yakin neman zaben Atiku, Segun Sowunmi.
Mahawara ta yi zafin gaske har ta kai ga rikidewa zuwa musayar kalamai ma su zafi da ta kusa kai wa ga bawa hammata iska.
Keyamo da Sowunmi sun ki yin shiru domin bawa dan jaridar gidan talabijin na Channels damar yi masu tambayoyi, lamarin da ta kai ga gidan talabijin din ya katse shirin ba tare da kammala shi ba.
Wannan mahawara mai zafi ta faru ne da safiyar yau a wani shiri da gidan talabijin din na Channels ke nunawa kai tsaye.
Tun bayan da Atiku ya lashe zaben cikin gida na jam'iyyar PDP ake musayar yawu tsakanin magoya bayansa da na shugaban Buhari, dan takarar APC.

Asali: Facebook
Ko a jiya sai da Legit.ng ta kawo maku labarin cewar dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana matakin da shugaba Buhari ya dauka na hana wasu mutane 50 fita daga Najerya da cewar tamkar mayar da Najeriya salon mulkin soja ne irin wanda shugaba Buhari ya yi a shekarar 1984.
DUBA WANNAN: Buhari ya fadi abin da zai faru ga duk malamin addinin da ya shiga hurumin siyasa
Jawabin da ofishin yakin neman zaben Atiku ya fitar a jiya, Lahadi, a Abuja, ya bayyana cewar duk da akwai bukatar hana aiyukan ta'addanci, amma dole a bi tsarin doka a duk abin da gwamnati za ta yi.
A cikin satin da ya gabata ne shugaba Buhari ya saka hannu kan wata doka da ta hana duk wasu mutane da ake tuhuma a kotu da laifin cin hanci da rashawa daga fita daga Najeriya.
Daga cikin mutanen da dokar ta shafa akwai tsofin gwamnoni 13 da ministoci 7, maza da mata.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng