Kasafin kudi: Za a saida wasu manyan kadarorin Najeriya – Inji Emefiele

Kasafin kudi: Za a saida wasu manyan kadarorin Najeriya – Inji Emefiele

Mun samu labari daga Jaridar The Cable Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya tabbatar da cewa Gwamnatin Najeriya ta shirya saida wasu manyan kadarorin kasar nan domin ta samu kudi.

Kasafin kudi: Za a saida manyan kadarorin Najeriya – Emefiele
Gwamnatin Najeriya za tayi gwanjon wasu kadarorin ta
Asali: Depositphotos

Godwin Emifiele a wajen wani taro da aka yi a Kasar Indonesiya ya bayyana cewa Najeriya za ta saida wasu kadarorin ta a shekarar nan. Emifiele yayi wannan bayani ne wajen wani zama da aka yi da Hukumar IMF mai bada lamuni ta Duniya.

Gwamnan babban bankin Najeriya da Ministan kasafi da ta kudi da ta tattali su na cikin wadanda su ka halarci babban wannan taro a Garin Bali da ke Kasar Indonesiya. CBN tace Hukumar ASCON ta shirya saida wasu kadarorin da Najeriya ta mallaka.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar a soma sayar da litar man fetur N205

A wajen taron da aka yi ne Gwamnan na CBN yake cewa Hukumar BPE za ta jagoranci saida wasu kadarori na Gwamnatin Najeriya domin a samu kudin da za a aiwatar da ayyukan kasafin kudin shekarar nan inda aka ware har Tiriliyan 8.6.

Wata babbar Jami’ar Hukumar SEC ta Najeriya Mary Uduk ta yi magana a wajen taron. Idan ba ku manta ba, kwanan nan ne dai mu ka ji cewa wata Kungiya ta ‘Yan kamashon Najeriya ta bayyana cewa za ta marawa Shugaba Buhari baya a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng