Kwankwaso ya hadu da Atiku Abubakar a gidan sa cikin dare

Kwankwaso ya hadu da Atiku Abubakar a gidan sa cikin dare

Mun samu labari daga Hon. Saifullahi Hassan wanda Hadimin Sanata Kwankwaso ne cewa ‘Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya gana da Sanatan na Kano a karon farko tun bayan da aka yi zaben fitar da gwani na PDP a makon jiya.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya hadu da Atiku Abubakar a gidan sa cikin dare
Kwankwaso ya taya Atiku murna bayan mako guda da zabe
Asali: UGC

A jiya ne Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara wajen 'Dan takaran Shugaban kasa a PDP Atiku Abubakar inda ya taya sa murnar nasarar da ya samu na rikewa PDP tuta a zaben 2019 ya kuma yi alkawarin mara masa baya a zabe na gaba.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da mutanen sa sun gana da Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ne a gidan sa da ke Unguwar Asokoro a babban Birnin Tarayya Abuja inda ya sha alwashin ganin PDP ta kai ga nasara a zaben da za ayi badi.

KU KARANTA: 2019: Manyan Kasar Ibo sun nuna tsagoron adawar su ga Peter Obi

‘Dan takarar na Shugaban kasa da ya sha kashi dai ya nuna cewa da shi da Mabiyan sa na Kwankwasiyya a fadin kasar nan za su ba Atiku Abubakar da Abokin takarar sa Peter Obi duk goyon bayan da ake bukata a shekara mai zuwa,

Wazirin na Adamawa Atiku Abubakar ya godewa Rabiu Kwankwaso wanda yace yana da karfi a tafiyar ta sa da ma Jam’iyyar PDP gaba daya. Sanata Kwankwaso dai ya gana da Atiku ne ‘Dan takarar Gwamnan Kano da kuma masu harin Majalisa a PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel