Dalilin da ya sanya Atiku ya zabi Peter Obi a matsayin Mataimakin sa

Dalilin da ya sanya Atiku ya zabi Peter Obi a matsayin Mataimakin sa

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Otunba Gbenga, jagoran kungiyar yakin neman zaben tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin da ya sanya aka zabi Peter Obi a matsayin wani zai yiwa Atiku mataimakin shugaban kasa.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Nation suka bayyana, a ranar Alhamis din da gabata tsohon Mataimakin shugaban kasa Atiku, ya zabi Peter Obi a matsayin Mataimakin sa bayan lashe tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a makon da ya shude.

Ko shakka ba bu Atiku da Peter Obi tsohon gwamnan jihar Anambra, za su riki tutar jam'iyyar PDP yayin babban zabe na 2019 inda za su fafata musamman da shugaban kasa Muhammadu Buharu na jam'iyyar APC.

Dalilin da ya sanya Atiku ya zabi Peter Obi a matsayin Mataimakin sa
Dalilin da ya sanya Atiku ya zabi Peter Obi a matsayin Mataimakin sa
Asali: Twitter

Cikin sanarwar da Gbenga ya bayyana a wannan mako, Atiku ya zabi Peter Obi a sanadiyar kuzarin sa irin na matasa gami da kwarewa da kuma masaniya akan tattalin arziki da a halin yanzu Najeriy ke da bukatar jagora mai makamanciyar wannan cancanta ta nagarta.

Tarihi ya bayyana cewa, irin wannan tafiya ta Atiku da Peter Obi tayi kamanceceniya da tafiyar tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari da kuma mataimakin sa, Marigayi Alex Ekwueme.

KARANTA KUMA: Dakarun sojin Najeriya sun yiwa 'Yan ta'adda na Boko Haram Ruwan Wuta a jihar Borno

Masana Alkuluma sun bayyana cewa, PDP ta bayar da wanna gurbi na kujerar mataimakin shugaban kasa ga yankin Kudu maso Gabashin kasar nan domin neman yarda da goyon bayan al'ummar kabilar dake korafin kowace gwamnati na mai she saniyar ware.

Legit.ng ta fahimci cewa, akwai dabara ta yiwuwar jam'iyyar PDP za ta zabo tare da nada wani gwamna na yankin Kudu maso Kudancin kasar nan a matsayin jagoran kungiyar yakin neman zaben kujerar shugaban kasa.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng