Zaben cikin gida: An yi takara tsakanin uwa da 'da a jam'iyyar APC

Zaben cikin gida: An yi takara tsakanin uwa da 'da a jam'iyyar APC

Hajiya Khadija Ibrahim, karamar ministar harkokin kasashen waje, ta kayar da Mohammed Ibrahim, dan mijinta, Bukar Abba Ibrahim, a zaben fidda 'yan takara na APC a jihar Yobe.

Khadija da Mohammed sun yi takarar neman kujerar majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar Damaturu/Gulani/Gujba/Tarmuwa a jihar Yobe.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Farfesa Abba Gambo, ya ce Khadija ta samu kuri'u 1,295 yayin da Mohammed ya samu kuri'u 15 kacal.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar duk kokarin shawo kan Mohammed domin ya janyewa Khadija, matar mahaifinsa, bai yi nasara ba.

Zaben cikin gida: An yi takara tsakanin uwa da 'da a jam'iyyar APC
Khadija Ibrahim
Asali: Facebook

NAN ta kara da cewa ragowar 'yan takarar kujerar biyu da suka hada da Abdullahi Kukuwa, dan majalisar dake kai yanzu, da Alhaji Ahmed Buba sun janyewa Khadija takarar da suka fito.

DUBA WANNAN: Hatsarin tankar dakon man fetur ya hallaka mutum 6, ya kone motoci masu yawa

Sanata Bukar Abba Ibrahim bai halarci ko daya daga cikin zabukan fitar da 'yan takara da aka yi a jihar Yobe ba, har wanda matarsa da dan sa suka fafata.

Sai dai wasu daga cikin daliget da suka halarci zaben sun yi alla-wadai da gazawar 'yan takarar na sulhunta kan su a cikin gida tare da bayyana cewar hakan ya nuna cewar akwai matsala a cikin gidan Bukar Abba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel