Amurka ta manta da sulhun ta da Koriya, an fara tsine-tsine daga Koriya

Amurka ta manta da sulhun ta da Koriya, an fara tsine-tsine daga Koriya

- An sha tata-burza tsakanin kasashen biyu

- An gana tsakanin shugabannin biyu a bana don sulhu

- Koriya tace Amurkar ta manta bata cire takunkumai ba

Amurka ta manta da sulhun ta da Koriya, an fara tsine-tsine daga Koriya
Amurka ta manta da sulhun ta da Koriya, an fara tsine-tsine daga Koriya
Asali: Facebook

A taron majalisar dinkin duniya dake gudana a Amurka a makon nan, kasar Koriya ta Arewa, wadda ke karkashin mulkin gurguzu na ilayan Kim Jong-Un shekaru kusan 60, wakilin kasar, Ri Yong Ho, wanda shine Ministan harkokin wajen kasar, ya koka kan takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasar sa.

A cewarsa, Amurkar ita ke hana ci gaba da sulhun zaman kasashen biyu kan tebur, da karfafa takunkumai duk da sulhun da ake kai.

DUBA WANNAN: Sai na zarce zaku san me ake kira aiki - Buhari

Ita dai Amurka ta yaki kasashen da ke bin gurguzu a shekarun baya, kuma ta raba koriyar biyu zuwa kudu da arewa, shekaru 60 da suka wuce.

An fara sulhu da Koriyar ta arewa mai fama da matsin tattalin arziki don ta hakura kar ta kera manyan makamai na kare daangi wadanda duniya ta hana amfani dasu.

Kasashe biyar ne kawai aka yarda su ajje makaman, Amurka, Chana, Rasha, Ingila da Faransa, kasashen da kuma ke kokarin nema a shekarun baya sun hada da Najeriya, Afirka ta Kudu, Libiya, Iraqi da Iran. Indiya, Pakistan da Israila tuni sun samu ta bayan fage.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel