Yajin Aiki: Shugaban Ma'aikatan Buhari ya gana da 'Kungiyar 'Kwadago

Yajin Aiki: Shugaban Ma'aikatan Buhari ya gana da 'Kungiyar 'Kwadago

Mun samu cewa a ranar Alhamis din da ta gabata ne Abba Kyari, shugaban ma'aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya a fadar shugaban kasa ta Villa dake babban birnin kasar nan na tarayya.

Ko shakka ba bu ganawar ta gudana ne domin tattauna al'amurra tare da neman kawo sulhu dangane da fusatar kungiyar da ta yi sanadiyar shiga yajin aiki na gargadi gadan-gadan da a halin yanzu ta tsayar da kasar nan cik wuri guda.

Shugaban ma'aikatan ya bayyana cewa, ya kirayi wannan ganawa domin tabbatar da lamarin da ya kawo dakacin gudanar sulhu na neman cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar akan mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan.

Yajin Aiki: Shugaban Ma'aikatan Buhari ya gana da 'Kungiyar 'Kwadago
Yajin Aiki: Shugaban Ma'aikatan Buhari ya gana da 'Kungiyar 'Kwadago
Asali: Depositphotos

A yayin ganawarsa da shugabannin kungiyar ya fahimci cewa, rashin cimma matsaya da kayyade sabon mafin karancin albashin ma'aikatan kasar nan ya haddasa wannan lamari na yajin aikin kamar yadda Kyari ya bayyana.

KARANTA KUMA: Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihar

Legit.ng ta kuma fahimci cewa, Kyari ya fayyace matsayar gwamnatin tarayya kan lamarin da ya shafin mafi karancin albashin ma'aikata ga shugabbanin kungiyar yayin ganawarsu da shugabanta na kasa, Ayyuba Wabba ya jagoranci wakilanta zuwa fadar shugaban kasa.

Sai dai cikin kyautata zato da kuma sa rai kungiyar ta bayyana cewa, za ta tuntubi sauraran rassan ta na kasa domin zayyana ma su yadda ganawarta da shugaban ma'aikatan ta kasance, inda za ta bayar da ta cewarta dangane da ci gaban yajin aiki ko kuma ta janye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel