Aisha Buhari tayi karin haske a kan rahoton sakin babbab dogarinta

Aisha Buhari tayi karin haske a kan rahoton sakin babbab dogarinta

Ofishin Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, ya karyata wasu rahotanni dake yawo a kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta kan cewar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun saki babban dogarinta da suka kama kwana biyu da suka wuce.

Suleiman Haruna, darektan yada labarai a ofishin Aisha Buhari, ne ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar ta shafinsa na Tuwita a yau, Alhamis.

“Har yanzu jami’an tsaro na cigaba da binciken Baban-Inna a kan manyan laifukan cin amana da cin hanci day a aikata.

Zai yi wuya hukumar DSS ta sake shi ba tare da kamala bincike a kan dukkan tabargazar day a aikata ba,” kamar yadda yake cikin jawabin.

Tun a ranar Tallata ne Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta nesanta kanta daga rahotanni dake yawo a kafafen yada labarai cewar ta bayar da umarnin tsare sarkin dogaranta (ADC), Sani Baban-Inna, bisa zargin yin amfani da sunanta wajen karbar cin hancin biliyan N2.5 daga hannun ‘yan siyasa da jami'an gwamnati.

Aisha Buhari tayi karin haske a kan rahoton sakin babbab dogarinta
Aisha Buhari
Asali: Depositphotos

Sai dai Aisha ta bayyana rashin jin dadinta bisa yadda babban dogarin nata, mai mukamin Safuritanda na ‘yan sanda, ke amfani da mukaminsa da kuma kusancinsa da ita wajen zambatar mutane, musamman ‘yan siyasa da jami’an gwamnati.

DUBA WANNAN: Yaki da cin hanci: Fayose ya yiwa Buhari tambayoyi 8 masu wuyar amsawa

Baban-Inna ya kasance babban dogarin Aisha tun shekarar 2016.

A jawabin da darektanta na yada labarai, Suleiman Haruna, ya fitar tun a ranar Talata, a Abuja, Aisha ta bayyana cewar kamun da jami’an tsaro suka yiwa Baban-Inna na cikin aikinsu da doka ta tanada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel