Sabon shugaban hukumar tsaro ta DSS ya ziyarci Buhari, hotuna

Sabon shugaban hukumar tsaro ta DSS ya ziyarci Buhari, hotuna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusif Magaji Bichi, da ya nada cikin makon jiya.

Bichi ya maye gurbin shugaban hukumar na rikon kwarya da aka nada bayan Osinabjo ya sallami tsohon shugaban hukumar, Lawal Daura, daga aiki.

Yusuf Magaji Bichi, sabon shugaban hukumar yan sandan farin kaya (DSS) ya kama aiki a hedikwatar hukumar domin tafiyar da shugabancin hukumar tsaron ranar juma'a.

Peter Afunanya, kakakin hukumar yace Bichi yayi jawabi ga ma’aikatan sannan ya nemi goyon bayan kowa da kowa dake aiki a hukumar DSS.

Kazalika ya sha alwashin yin aiki tare da su a matsayin tawaga guda. Sannan ya kara da cewar manufarsa shine yin aiki yadda ya kamata domin inganta hukumar DSS da kuma tabbatar da jin dadin ma’aikatan hukumar.

Sabon shugaban hukumar tsaro ta DSS ya ziyarci Buhari, hotuna
Buhari da Bichi
Asali: Twitter

Sabon shugaban hukumar tsaro ta DSS ya ziyarci Buhari, hotuna
Sabon shugaban hukumar tsaro ta DSS ya ziyarci Buhari
Asali: Twitter

Bichi ya kuma bayar da tabbacin cewa zasu ba gwamnati cikakken goyon baya wajen sake gina tattalin arziki, tabbatar da tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Ya kuma bukaci ma’aikatan da su gudanar da aiki akan wannan tafarki. Ya kuma bukaci da su mutunta doka tare da daraja yancin dan Adam.

DUBA WANNAN: Sojoji sun bazama neman janar da ya bace a Jos kwana uku bayan ya yi ritaya

A baya Legit.ng ta rawaito cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba, ya bayyana Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon darakta-janar na hukumar yan sandan farin kaya (DSS).

Sabon shugaban zai karbi aiki daga hannun Matthew Seiyeifa, wanda ya maye gurbin Lawal Daura da aka sallama daga aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel