Dan takarar da ya kamata PDP ta tsayar muddin tana son kada Buhari - Makarfi

Dan takarar da ya kamata PDP ta tsayar muddin tana son kada Buhari - Makarfi

- Jigo a jam'iyyar PDP, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya ce dole PDP ta tsayar da dan takara mai nagarta muddin tana son kada Buhari

- Makarfi kuma ya ce ya fita daban cikin sauran 'yan takarar saboda kwarewarsa da nasarorin da ya samu a mukamman da ya rike a baya

- Ya kuma ce zai goyi bayan duk wanda jam'iyyar ta tsayar muddin shi jama'a suka zaba

Tsohon Ciyaman din riko na jam'iyyar PDP, kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, ya ce dole PDP ta tsayar da dan takara mai nagarta, gaskiya da rikon amana muddin tana son kayar da Buhari a zaben 2019.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna, ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da ya yi da jaridar Leadership. Ya kuma yi fashin baki kan wasu batutuwa masu alaka da zabe.

Dan takarar da ya kamata PDP ta tsayar muddin tana son kada Buhari - Makarfi
Dan takarar da ya kamata PDP ta tsayar muddin tana son kada Buhari - Makarfi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Danwaken zagaye: An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Shekarau da Ganduje

Makarfi ya ce ya yanke shawarar shiga takarar shugabancin kasar ne saboda kwarewarsa da irin nasarorin da ya samu a ayyukan da ya yi a baya. Ya bayar da misalin yadda ya ja ragamar mulkin jihar Kaduna inda ya magance matsalar tsaro ya kuma dai-daita tsakanin jama'a mabanbanta addini da kabila a jihar.

Sanata Makarfi kuma ya ce ya banbanta da sauran masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a PDP saboda irin gwagwarmayar da ya yi na tabbatar da cewa jam'iyyar bata ruguje ba lokacin da aka bashi rikon kwarya. Ya ce wasu sun taimaka masa amma a matsayinsa na shugaba shine nauyin ya rataya a kansa.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa ana gab da kulla yarjejeniya tsakanin Mallam Ibrahim Shekarau da jiga-jigan jam'iyyar APC. Ana sa ran idan tattaunawar tayi armashi Shekarau zai sauya sheka zuwa APC sakamakon rikicin da ya barke a PDP ta Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel