Osinbajo ya karbi bakuncin 'yan matan Najeriya da suka yi bajinta a Amurka
A yau, Alhamis ne, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya karbi bakuncin wasu 'yan mata da suka nuna bajinta a bangaren fasaha a kasar Amurka.
Osinbajo ya karbi bakuncin tawagar 'yan matan a fadar gwamnatin Najeriya dake Abuja.
'Yan matan da ake kira "Team Save-A-Soul" sun zama zakara a wata gasa ta kasa a kan fasahar zamani da aka yi a kasar Amurka.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: An kama wani mutum da ya kira shugaban kasa biri

Asali: Twitter
'Yan matan sun samu rakiyar shugaban hukumar bunkasa sarrafa fasahar zamani ta kasa, Dakta Aliyu Pantami.

Asali: Twitter
A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta kawo maku kun ji cewar kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewar zata bayar da tallafin kudi maras riba ga kananan 'yan kasuwa.

Asali: Twitter
A yayin ziyarar, Osinbajo, ya zagaya tare da ganawa da 'yan kasuwar da kuma yi masu tambayoyi.
'Yan kasuwar sun nuna matukar jin dadinsu da ziyarar ta Osinbajo da kuma yadda ya saki jiki da su.
Da yake jawabi ga 'yan kasuwar, Osinbajo, ya ce "tallafin na kanana ne ba manyan 'yan kasuwa ba. Zamu raba N10,000, duk wanda ya biya bayan wata 6 zai samu bashin N15,000, wanda idan mutum ya biya sai ya samu bashin N20,000."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng