Kalli kwararren telan Najeriya daya dinka ma shugaban kasar Birtaniya riga (Horuna)

Kalli kwararren telan Najeriya daya dinka ma shugaban kasar Birtaniya riga (Horuna)

Jama’a da dama sun nuna sha’awarsu ga kwalliyar da shugaban kasa Birtaniya, Theresa May ta yi da wata rigar sama da sanya a yayin ziyarar da ta kawo Najeriya a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta.

Sai dai abin da jama’a da dama basu sani ba shine wannan riga an dinka shi ne a Najeriya, a shagon wani matashi da yak ware a harkar dinky, wannan yasa jaridar thecables ta kwakulo wannan matashi mai suna Emmanuel Okoro.

KU KARANTA: Rabonsu ya rantse: Gwamnatin jahar Kaduna na neman teloli don ta basu kwangila

Kalli kwararren telan Najeriya daya dinka ma shugaban kasar Birtaniya riga (Horuna)
Okoro da Theresa
Asali: Depositphotos

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Okoro ya bayyana kansa ne a shafin kafar sadarwar zamani ta Instagram, inda ya bayyana godiyarsa tare da mutunta shi da shugaban Birtaniya ta yi ta hanyar sanya rigar daya dinka mata.

Emmanuel Okoro wanda ya bude kamfanin dinki maisuna Emmy Kasbit a shekarar 2014, yace ya samu damar zama da Theresa a yammcin Laraba, inda suka tattauna batutuwa da dama da suka shafi tallafa ma mata.

Kalli kwararren telan Najeriya daya dinka ma shugaban kasar Birtaniya riga (Horuna)
Theresa da Buhari
Asali: Depositphotos

A shekarar 2017 ne ya lashe kyautar ‘Fashion Focus Prize’ a jihar Legs, inda ya samu kyautar kudi dala dubu goma sha uku da dari tara ($13,900), sa’annan mataimakiyar bankin Amurka Merril Lynch ta bashi horo akan dabarun kasuwanci.

Shi dai Okoro yana amfani ne da atamfofi wajen dinke dinken kayan mata da maza daga cikin wadanda suka sanya kayan da Okoro ya dinka akwai fitacciyar marubuciya Chimamanda Adichie, shahararrun mawakan Najeriya Flavour da Adekunle Gold.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel