Yadda Daliban Jami'a 7 Suka Rasu ana tsaka da Bikin Kammala Karatunsu

Yadda Daliban Jami'a 7 Suka Rasu ana tsaka da Bikin Kammala Karatunsu

  • An shiga jimami a Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) bayan rahotannin mutuwar wasu dalibai bakwai da suka kammala karatu
  • An ce lamarin ya faru ne a daren Laraba a wani gidan haya da ke yankin Hilltop, inda daliban suka shirya liyafar murnar kammala karatunsu
  • Har yanzu ba a tabbatar da musabbabin mutuwarsu ko sunayen wadanda suka rasu ba, yayin da jami’ar ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nsukka – Rahotannin mutuwar wasu dalibai bakwai da suka kammala karatu a Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) sun jefa al’ummar jami’ar cikin jimami.

An ce lamarin ya faru ne a daren Laraba a yankin Hilltop, wani wurin zaman dalibai da ke wajen harabar jami’ar a Nsukka, jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta

Kofar shiga jami'ar UNN
Kofar shiga jami'ar UNN da ke Enugu. Hoto: UNN
Source: UGC

Rahoton Vanguard ya nuna cewa daliban sun taru ne a wani gida domin gudanar da liyafar murnar kammala karatunsu, amma bikin ya rikide zuwa abin takaici.

Yadda daliban suka mutu

Kafin faruwar lamarin, daliban sun wallafa hotuna da bidiyoyi a kafafen sada zumunta, inda suke nuna farin cikinsu bayan kammala karatunsu.

Sai dai an ce bikin ya rikide zuwa mummunan lamari, bayan samun rahotannin mutuwar daliban bakwai a wurin taron.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa abin da ya faru ya zama wani mummunan yanayi ga al’ummar Nsukka.

A cewarsa, daliban sun rasa rayukansu ne a wani liyafar cikin gida da aka shirya domin murnar kammala karatunsu.

Taswirar jihar Enugu
Taswirar jihar Enugu a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ba a gano dalilin mutuwar ba

Wasu bidiyoyi da suka bazu a kafafen sada zumunta sun nuna gawarwakin wasu mutane kwance a cikin wani babban daki, amma har yanzu ba a tabbatar da sahihancin cikakkun bayanan da ke tattare da hotunan ba.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisa ya ga ta kansa da ya yi ƙokarin tallata Tinubu a taron jama'a

Musabbabin mutuwar daliban bai fito fili ba, haka kuma ba a tabbatar da sunayen wadanda suka rasu a hukumance ba.

Wani rahoto da wani dalibi a jami’ar ya bayar, shi ma ya nemi a sakaya sunansa, ya yi zargin cewa binciken lafiya da aka yi wa daya daga cikin wadanda suka tsira ya nuna yawan kwayoyin maye a jikinsa.

Sai dai wannan bayanin bai samu tabbaci daga hukumomin lafiya ko jami’an tsaro ba, inda ake jiran jin me za su fada game da lamarin.

Jami’ar UNN ba ta yi magana ba

A lokacin hada wannan rahoto, mahukuntan Jami’ar Najeriya da ke Nsukka ba su fitar da sanarwa kan lamarin ba.

Rahoton the Sun ya nuna cewa rundunar ’yan sandan jihar Enugu ba ta tabbatar da faruwar lamarin ko bayyana matakan da ta dauka ba.

Daliban ABU sun nuna bajinta

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) sun kera wata sabuwar sandar zamani domin taimaka wa mutanen da ba sa gani wajen tafiya cikin sauki.

Kara karanta wannan

Yadda aka shigo da tarin makamai Najeriya ana shirin zaben 2027

Na’urar tana amfani da na’urorin gano cikas, ramuka da ruwa, inda take gargadin mai amfani ta hanyar girgiza da sautuka daban-daban.

Sandar ta kuma kunshi katin SIM da ke ba mai amfani damar aika sakon SMS zuwa ga wanda aka sanya a matsayin mai kula da shi, domin taimaka masa samun agaji idan bukatar hakan ta taso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng